TSAKURE.
Wannan Takarda insha-Allahu za ta yi duba akan
Hanyoyin yaxuwar Cutuka a mahangar muslunci,
da matakan kariya, ma'anar Annoba a taqaice,
sabubbanta, da yadda magabata suke magance ta,
yayin da ta taso.
Haka kuma takardar za yi waiwaye akan tasirin Abinci,
tsirrai, a zamanin magabata, wajan magance Cutuka.
SHIMFIXA
GABATARWA.
Ina godiya ga Allah mai girma da xaukaka, Allah ya yi daxin tsira ga fiyayyen halitta Manzan tsira Annabir-rahma (SAW).
Matashiyar da aka ba ni domin na yi bayani akanta tana da faxi kuma maudhu'in da aka ba ni guda shida ne a guda xaya, misali:-
YAXUWAR CUTUKA A MAHANGAR MUSLUNCI DA MATAKAN KARIYA, ANNOBA, NAU'O'INTA, SABUBBANTA, TARIHINTA, DA YADDA MAGABATA SUKE MAGANCE TA. SAI RIGA-KAFI.
Me ne ne Ma'anar Cuta? Ya take yaxuwa?
Cuta I tace: Duk wani abu Zai canza Jiki, ya fitar da shi daga Dabi'arsa ta Alasali, Ko ya jefa jiki cikin furgici da razani. {kitmer 2018}.
Wasu Masana kuma suka ce: "Cuta it ace: "Canzawar yanayin aiyyukan jiki ko wata gava, kafin yin magani." {pph&s Abbaza 2006).
HANYOYIN SAMUWAR CUTA DA YAXUWAR TA.
Hanyoyin samuwar cuta suna da yawa, kuma akwai maganganun Masana masu yawa akan hanyoyi samuwar cutuka. Malam Mustapha haqqiy a cikin littafinsa mai suna:- raddul-bala, birruqya ash-shar'iyya. Ya ce:-
Hanya ta far ta samuwar Cutuka ga Al'umma, it ace:-
Qaddarawa ta Ubangiji. Kamar yadda ya faxa cikin surah al'hadi/ 22.
ﭧ ﭨ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭽ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﭼ الحديد: ٢٢
Haka ya faxa a ckin suratuttaubah/23.
ﭧ ﭨ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭽ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﭼ التوبة: ٥١
Baiyyanar Zinace-zinace (Afasha).
Kanar yadda ya zo a cikin Hadisin Abdullahi Xan Umar wan Ibni. Majah ya ruwaito cewa: manzan Allah. (SAW) Y ace:-
(يَا مَعْشَرَ الْمُهَاجِرِينَ خَمْسٌ إِذَا ابْتُلِيتُمْ بِهِنَّ وَأَعُوذُ بِاللَّهِ أَنْ تُدْرِكُوهُنَّ لَمْ تَظْهَرْ الْفَاحِشَةُ فِي قَوْمٍ قَطُّ حَتَّى يُعْلِنُوا بِهَا إِلَّا فَشَا فِيهِمْ الطَّاعُونُ وَالْأَوْجَاعُ الَّتِي لَمْ تَكُنْ مَضَتْ فِي أَسْلَافِهِمْ الَّذِينَ مَضَوْا....
(Assabti 2008.)
Yawaitar Zunubai ga Al'umma.
Kamar yadda ya faxa a cikin surah/30
ﭧ ﭨ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭽ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﰁ ﰂ ﰃ ﰄ ﰅ ﰆ ﰇ ﭼ الشورى:٣٠
فعن أبي سعيد وأبي هريرة -رضي الله عنهما- عن النبي ﷺ قال:
"ما يصيب المسلم من نَصَب، ولا وَصَب، ولا هم، ولا حزن، ولا أذى، ولا غم، حتى الشوكة يشاكها إلا كفر الله بها من خطاياه[1].
"Babu wani abu da zai sami Musulmi na gajiya, da cutuka, da damuwa da vacin rai, ko wani abu ya same shin a cutuwa ko na bakin ciki, kai har da qaya ya ke takawa, har sai Allah ya gafarta masa kura-kuransa da ita." (Assabti.2008.gogle)
Amma su masu kimiyyar zamani musamman masu ilimin qwayoyin cuta suna ganin cutuka gabaki xaya suna samuwa ne sakamakon rayuwar qananan halittu. (microorganisms), wato wasu qananan halittu masu rai waxanda ido bay a iya ganin su, said a mudubin ganin qurulla na likitoci, kuma sun kasa su izuwa rukuni biyar kamar haka:-
VIRUS
BACTERIA.
PROTOZOA.
FUNGI
ALGAE.
Sannan kowanne xaya cikin waxannan rukunai yana da rassamai yawa a qarqashinsa. (kitmer.2018).
Haka kuma Ibn. Qaiyyum a cikin Axxibbun-nabawiy ya \ce:
"Cutuka iri biyu ne kamar haka:
Me kama jiki, da
Me kama zuciya.
Masu kama zuciya iri uku ne, su ne:
Cuta ta sha'awa.
Cuta ta munafirci da son zuciya.
Cuta ta shakku da kokwanto.
FAXAKARWAR ANNABI (SAW). GA YAXUWAR CUTA.
Annabi (SAW) ya ba da haske game da yaxuwar cuta kamar haka:-
Ta hanyar Karnuka.
Ta hanyar Quda
Ta hanyar Saduwar Aure Miji da Mata.
Ta hanyar Hassada/kambun ido.
Ta hanyar barin moxa bude bude…....ds.
MA'ANAR ANNOBA.
Za mu xauki Hadisin Assaiyidah Aisha (RA) wanda Imamul Bukhari ya ruwaito (3474). Shaikh Usaimin ya yi sharhi akan wannan Hadisi, sannan Dr. Khalid bin Usman Assabtiee a cin sharhi Riyadhussalihin ya yi Karin haske akan wannan Hadisi, cewa: ta tambayi Annabi (S.A.W.) Me nene Annoba?. Sai ya ce: "Annoba azaba ce da Allah yake saukar da ita ga wadannda yake so daga cikin Bayinsa, kuma ya sanya ta zama rahama ga Bayinsa Muminai, ba wanda za ta same shi, ya zauna a gurin da ta same shi bai fita ba da nufin neman lada, to, idan ya mutu a sanadiyar wannan Annoba hakika ya yi mutuwar shahadah.
Haka kuma Annoba tana nufin samuwar wasu kwayoyin Cuta masu saurin yaduwa kuma masu saurin halaka Dan-adam.
Annaoba ba sabon abu ba ne a gurin Musulmi. Tana faruwa sakamakon abubuwa da dama kamar haka:
Karnuka,
Kudaje,
Beraye, da
Aladu.
Tsintsaye, da sauransuyayi.
Kamar na yi bayani a baya Allah yakan saukar da Annoba ga Al'umma idan Zunubin su ya yawaita.
Yana daga cikin koyarwar sa (SAW) cewa:- Idan Annoba ta faru gari, wanda ke ciki kada ya fita, wanda yake waje kuma kada ya shigo.
Kamar abin da ya faru zamanin khalifa Umar bin khaddab yayin da ya yi tafiya da Jma'arsa zuwa Sham, sai aka ba shi labarin akwai Annoba a kasar, sai ya zabi wadanda suka halarci yakin Badar yayi zama da su, ya shawarce su akan su shiga ko kada su shiga, sai, Jama'a ta kasu biyu, Wasu daga cikin suka ce a shiga, Wasu kuma suka ce kada a shiga, Abdurrahman bin Auf ya xan fita zuwa wata buqa ya dawo sai ya tarar da suna wannan muhawara, sai ya tuna musu wancan Hadisi… sai dukkan su suka amince da kada a shiga, khalifa Umar ya yarda da shawarar su, suka juya ba su shiga ba.
An yi wata Annoba a zamanin Saiyyina Umar yana khalifa Ana kiran wannan annoba da:- (AMWAS) . ta faru ne a shekara ta sha takwas (18) bayan hijira dai-dai da (640), miladiyya. Bayan an bude Baitil-mukdis. Sahabbai da dama sun yi wafati a sababin wannan annoba.
An kira wannan annoba da suna (AMWAS) ne, saboda annobar ta wannan garin ta fara.
Amwas wani kauye ne karami a kasar Falasdinu, yana tsakanin ramla da baitil makdis. Daga kauyen Amwas cutar ta fara, bayan ta gama da kauyen, daga nan ta watsu zuwa garuruwan kasar Sham. Shi ya sa ake kiran ta da sunan wannan gari (AMWAS).
Haka kuma kasar Isra'ila ta taba rusa garin, ta mai da shi Kufayi, a (1967). Ta kashe kudi ta tsara shi, a matsayin gurin yawon shakatawa, ta kuma canza masa suna ta ya koma (KANADA).
MACE-MACE DA AKA YI A ANNOBAR AMWAS
Malam Wakidi ya ya ce:-
" Yawan Musulmin da suka rasu a wannan Annoba, ya kai Mutum dubu ishirin da biyar (25000-00), Wasu kuma sun ce: yawan Mutanen da suka Mutu sun kai dubu talatin. (30,000.)
Manyan Sahabban da suka rasu a wannan Annoba sun hada da:-
Abu-ubaidah bin Jarrah, Ma'azu bin Jabalin, Yazidu bin Ma'awiyya, da Suhail bin Amru. Sauran sun hada da Dhirar binl-azwar, Abu Jundul bin Suhail. Da sauran Manya-manya daga cikin Sahabbai, shi ya sa ake kiran wannan shekara da:- (AMURRAMAD) Wato shekarar Qurmis, ko shekarar Toka. Saboda gwarazan Mutanan da aka rasa a cikinta.
Ibni Hajar ya ce:- "Annobar Amwas ta faru ne a shekara ta 18. ga hijra, kuma Mutane (25,000=00) ne suka rasu ta dalilinta.
Imamuxxabriy a cikin Kitabut -tarikh ya ce:- "Akwai sabanin fahimta na Malamai akan shekarar da aka yi annobar Amwas, wasu na ganin tun da an shiga shekara ta (18) ga hijra to ke nan a ita aka yi ta. Cikin wadanda suka rasu akwai: Haris bin Hisham, da Utbatu bin Suhail, ds.
ANNOBAR COVID 19
Halittar qwayar cutar "Corona"
Akwai wani bayani mai qayatarwa akan cutar corona, da wani Malami mai suna (Hafiz Koza), ya sa shi a yanar gizo. Kuma ya ce: wata Jami'a ce ta fitar da shi, (Johns Hopkins) shi kuma ya fassara shi zuwa Hausa tare da taimakon Mai Girma Galadiman Daura Hakimin Mai'aduwa, Alhaji Ahmad. Kamar yadda ya faxa.
Abubuwan da suka faxa suna da yawa amma zan xauki kadan in taqaita su saboda lokaci.
1. Kwayar cutar korona (Coronavirus) ba rayayya ba ce, wani dan karamin sinadarin furotin ne lullube da mayanin kakidi (maiko), shi ya ke ba ta kariya, da zarar ta shiga jiki ta kafar da ke da lema kamar: Ido, hanci, baki, ds. Sai ta gwamutsa da tubalin ginin halittar jiki (body cells), sannan ta sauya kama ta zama fitinannun qwayoyin cuta masu saurin rivanya da kai farki ga jiki.
Abin dubawa shi ne:
Qwayar covid 19. Ba rayaiyiya b ace.
Ba ta mutuwa da garaje.
Tana da saurin rugujewa.
Xabi'ar cutar sanyi da bushi.
Ruwa da kumfan sabulu na iya ruguza ta.
Idan zafi ya narka mayanin maikon day a rufe ta, za ta iya rugujewa.
Amfani da ruwa mai xumi ta fiskar wanke hanu, wanka,ko shan shayi, yan da tasiri akan cutar.
Tana rugujewa a jikin tufafi bayan awa uku. In ba a kada shi ya fantsam ga jama'a ba. Ds.
HANYOYIN DA ZA A HANA YAXUWAR CUTAR COVID 19.
Hanyoyin su ne:-
Tsoron Allah, kiyaye dokokinsa, da komawa zuwa gare shi.
Amfani da hanyoyin kiwo lafiya da Malaman Muslunci suka bayar.
Dagewa da karanta Al'qur'ani, azka, da Addu'o'i.
Nasantar duk wani da ka iya kawo faruwar cuta.misli:-
Murhu uku.
Mai masaukin cutar (Hos)
Gurin zama.
Abin day a jawo ta. (pphps Abbazah 2008).
Abinci mai gina jiki. (Azka xa'aman). (Aburrub. 2003}
KAMMALAWA.
Anan zan dakatar da 'yar wannan Takarda tare da godiya ga Allah da ya ba ni ikon kamala ta cikin halin lafiya, ina yaba wa 'yan lajnatud-da'awa da suka shirya wannan bita, dukkannin waxanda suka ba da gummawa ta kowacce irin hanya Allah ya saka masa da mafficin alkhairi. Ameen.
MANAZARTA
Alqur'ani Mai Girma.
Alqurxubi (2003) Aljami'u Li-Ahkamil Qur'an Dar
Alhadith.
Axxabari Jami'ul Bayan Fi Ta'awilil Qur'ani.
Attaufiqiyya Misra.
Ahmad Yusuf Alhaji (2003/1424): Al'i'jaaz Al-Ilmiy Fil Qur'anil Karim Wassunnatul Muxahhara.
AbdulFatah Aiman (2004/1425): Min Sahihix
xibbin Nabawiyya: Asshifa'u Min wahyi Khatimil Anbiya'i.
Mubadi'u fissihati wassalamatul-al'ammah.
-Dar-al'maisarah
Al'giza'u wal-mautul baxe'ee. Dr. Mahmud. Aburrub. Darul-kutubul al'ilmiyyah Bairut labnan.2003=1424.AH.
Ustaz Muhammad Abdurrahman, Addibbul-Mujarrab: {2001:3/8
Dr. Mustapha Muhammad Azzahbiy. Naqalul a'dha'a bainaxxibbi waddeni. 1993.
Dr. Garba Iliyasu (MBBS,FMCP) Na Sashen Cutuka masu yaxo Tsangayar Horar da Likitoci Jami'ar Bayaro kano.
Malam Umar Nadim Qiblami
Minnaturrahman Fi Ba'adhi Asrarul Qur'an.
2013=1434AH
Alhamdu lillah.