Sunday, 22 December 2013
Addu'ar razana ko kasa Barci.
" Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushinsa, da ukubarsa da sharrin Bayinsa da kuma zungure-zunguren Shaidanu da za su halarto ni."
Monday, 20 May 2013
Sunday, 19 May 2013
TAKAITACCEN TARIHIN KACHAKO
TAKAITACCEN TARIHIN KACHAKO
A WURIN BIKIN KARRAMA MAIGIRMA DAGACIN KACHAKO ALH. YUNUSA IBRAHIM, SABODA KAMMALA AIKIN GWAMNATI DA YA YI
RANA: ASABAR 11/05/2013
LOKACI: 10 NA SAFE
WURI: MAKARANTAR
‘YAN MATA TA WRECA (GGASS, KACHAKO)
MAI GABATARWA
(DR.) YAKUBU MAI GIDA KACHAKO
2013/1434 AH
KAFUWAR GARIN KACHAKO
Sannen abu ne a rayuwar Al’umma sukan shugabantar da wani
mutum a kansu, wala’Allah ko dan karfi, jarumta, dukiya, ilimi, ko kuma don
wata Baiwa da Allah ya yi masa. Wannan ce ta sanya Mal. Abubakar Mutumin Qasar
Bebeji, Bafulatani, makiyayi, wanda aka fi sani da: “Jauro Buba Fange” ake yi
masa kirari da cewa shi ne farkon wanda ya sari garin Kachako.
Masana tarihi sun ce lokacin da Jauro Buba Fange ya sauka
a wani Daji mai cike da Bishiyoyi da Itatuwa, da Tsirrai, da Dausayi, gurin ya
yi kacha kacha da bishiyoyi, kuma Dajin yana dauke da Namun Daji kamar irinsu Kura,
Zaki, da sauran kananan Dabbobi, a wannan gurin ya sauka tare da Dabbobinsa.
Saboda gudun kada Dabbobin Daji su din ga yi musu barnar Dabbobinsa ya sa bayan sunsare
manyan Bishiyoyi, kananan bishiyoyin suka fiffike kansu suka yi musu tsini
domin idan Dabbobin Daji sun kawo bara suka kore su sai su dinga sossokewa da
wannan tsinin itatuwan, wannan ne yasa lokacin da yan’uwansu suka zo sai suka
ce: “waxannan itatuwan fa kacho kacho ga kuma guri yayi kacha kacha?” an ce
daga wannan tambayar ne aka samo asalin sunan KACHAKO. Kuma ance amsar
da suka ba su yayin da sukayi musu wannan tambaya itace: “muyi hakuri mu
dangana, bamu san abun da Allah zai yi ba sababin zamanmu a wannan wuri”. An ce daga wannan kalmar ne
aka sanya wa unguwar da Jauro Buba ya sauka sunan MADANGANA.
GARURUWAN
DA SUKA YI IYKA DA KACHAKO
Yamma
|
Arewa
|
Gabas
|
Kudu
|
Durbunde (2.0 nm)
|
Tsangaya (5.8 nm)
|
Kogin Huguma (3.6 nm)
|
Iggi
(5.0 nm)
|
ASALIN SARAUTAR KACHAKO
Masana tarihi na
cewa:- Asalin waxanda suka sari garuruwan:
Kachako, Garko, Toranke
da Kibiya, Mutanen Qasar Bebeji ne, kuma
Sarkin Bebeji ya xauki lokaci mai tsawo yana zuwa kachako domin karvar harajin
da aka tattara na jama’ar garin kachako.
Kamar yadda mukayi
bayani a baya cewa al’umma sukan shugabantar da wani daga cikin su saboda wata Baiwa
da Allah ya yi masa, to haka wannan abu ya faru bayan Jauro Buba da Iyalansa
sun zauna a wannan guri sun yi sansani,
sai ya tafi kasar Bebeji ya sayo Bawa mai suna Mal. Abubakar, ranar da
aka kawo shi sai ya kwana yana karatun Alqur’ani, da gari ya waye sai Jauro
Buba ya zo ya tsugunna a gabansa ya ce da shi: “ka yi hakuri! Wallahi ban san
kai malami ba ne, kuma daga yau na yanta ka, ka zama Xa”. Daga nan sai ya naxa
shi limanci, jagorancin al’umma da karantarwa ya daura auren ‘yar sa ya ba shi,
ya kuma tura masa ‘ya’yansa guda uku
domin ya karantar da su, su ne:
1.
Fyati
2.
Jexi da
3.
Yunusa
Wannan Bawa mai
suna Mal. Abubakar wanda aka ‘yanta kuma aka ba shi jagoranci da limanci da
karantarwa, shi ake kira: LIMAN YARO kuma shi ne ya ci gaba da shugabancin
jama’a, da yi musu limanci har bayan barin Jauro Buba duniya. Wannan shi ne matakin
farko na shugabanci a garin Kachako, ke nan shugabanci a garin kachako ya fara
ne da Limanci ba da Dagaci ba.
Bayan rasuwar
Liman Yaro sai aka naxa FYATI a matsayin limami, shi ne liman, shi ne
shugaban jama’a, kuma shi ne babban Xan Jauro Buba wanda ya yi karatu a hannun
Liman Yaro, ya ci gaba da jagorancin jama’a kuma yana yi musu Sallah.
Bayan Liman Fyati
ya kau sai aka naxa JEXI a matsayin liman kuma shugaban jama’a yayi wa
mutane limanci kuma ya shugabance su a cikin al’amuran rayuwa.
Bayan Liman JEXI
ya kau sai aka zavi YUNUSA domin ya gaji Jexi, da shugabanci ya zo kan
Yunusa sai ya ce shi Dagaci ne ba Liman ba, don haka daga kansa ne aka daina
haxa shugabanci da limanci ga mutum xaya a ka ware Dagaci da ban Limamin gari
da ban.
Waxanna sune
shugabanni guda uku da suka fara shugabantar garin Kachako.
GA JERIN SUNAYEN
WAXANDA SUKA SHUGABANCI GARIN KACHAKO A TAIQAICE
1.
Mal. Abubakar (Liman Yaro) Limanci
2.
Fyati Limanci
3.
Jexi Limanci
4.
Yunusa Dagaci
5.
Muhammadu Tukur Dagaci
6.
Turaki Dagaci
7.
Maina Bawa Dagaci
8.
Xan Tsoho Dagaci
9.
Qarfawa Dagaci
10.
Alhaji Dagaci
11.
Yunusa Dagaci
12.
Sulaimanu Dagaci
13.
Usmanu Dagaci
14.
Ibrahim Dagaci
15.
Iro Dagaci
16.
Indabo Dagaci
17.
Ilu Dagaci
18.
Ali Dagaci
19.
Mamuda Dagaci
20.
Sulaimanu (Na Qwara) Dagaci
21.
Haruna Dagaci
22.
Langwami Dagaci
23.
Bashari Isma’il Dagaci
24.
Alh. Yunusa Dagaci
Masana tarihi sun
ce Dagatai uku ne suka mulki kachako ba daga jinin fulanin kachako ba su ne:
1.
Turaki
2.
Indabo da kuma
3.
Alhaji Muhammadu (Langwami)
KARIN BAYANI
DAGACIN KACHAKO QARFAWA
Shi ne vangaren su Alh. Uba Saraki da ‘yan’uwansa
DAGACIN KACHAKO ALI
Tun daga lokacin da aka yaye shi mahaifiyarsa ta tafi da shi
garin VAGWARO bai dawo kachako ba sai da sarauta.
DAGACIN KACHAKO SULAIMANU
Shi ne kakan su Mal. Bello
DAGACIN KACHAKO USMANU
Shi ne Baban su Mal. Bello Uban Mal. Hassan Buyuta.
DAGACIN KACHAKO IBRAHIM
Shi ne Uban Dagacin Kachako Mamuda
DAGACIN KACHAKO IRO
Shi ne Jikan Fyati dan Liman Abubakar Mai gidan vaure,
kuma shi ne uban su Liman Mal. Sule, Mal. Lurwanu, Alh. Inuwa Na Atsakiya, Mal.
Amadu, kuma shi ne kakan su Mal. Rabi’u Inuwa.
DAGACIN KACHAKO MAMUDA
Xan Dagacin Kachako Ibrahim
DAGACIN KACHAKO YUNUSA
Shi ya haifi Qwara, ita ce kuma ta haifi Dagacin Kachako
Sule wanda ake ce masa Sulaiman na Qwara, kuma shi ya haifi Dagacin Kachako
Haruna da kuma Dagacin Kachako Al’haji Yunusa wanda ake yin wannan taro sabo da
shi.
SANA’O’IN JAMA’AR KACHAKO
Al’ummar garin kachako suna da sana’o’i da suke gudanar
wa domin su nemawa kan su abubuwan masarufi.
Man yan sana’o’in su su ne:
1.
Noma
2.
Kiwo
3.
Dukanci
4.
Qira
5.
Sassaqa
6.
Wanzanci
7.
Rini
8.
Ginin tukwane
9.
Kaxi
10.
Awon Gyaxa da kuma awon Fata da sauran su.
RINI
Kachako ta shahara a wajen sana’ar Rini, shi ne ya sa ma
muke da manyan wuraren rini da ake kiransu Karofi kamar haka:
1.
Karofin lemo
2.
Karofin gwada
3.
Karofin bayan gidan Ali Batsiya
4.
Karofin bayan makarantar GGC da kuma
5.
Karofin maza tsaye
An kira gurin da wannan suna maza tsaye saboda
wata rana Ningawa (Mutanen Ningi) sun shigo yaqi garin kachako sai suka tarar
da marina suna ta aiki, sai suka sossoke su da mashi suka jefa su a cikin rijiyoyin
rini, to wannan lokacin ne sai aka tura mayaqa suke tsaiwa a kansu da kayan
yaqi su kuma suna aikinsu, domin da mahara sun hango mayaqa sai su juya da gudu.
Wannan dalili ne ya sa ake kiran wannan guri da suna MAZA TSAYE kuma har yanzu
akwai rijiya a gurin da ake kiranta da suna maza tsaye.
ASALIN KALMAR FANGE
Anayiwa Jauro Buba laqabi da Fange, dalilin yi masa laqabi
da wannan suna shi ne, su fulanin da ke tare da shi suna daukar sa a matsayin
uba ko baffa don haka idan za su kira shi sukan ce da shi BAFFANGE da ga
nan ne aka ci gaba da kiran sa Fange maimakon Jauro Buba Baffange.
KIRARIN DA AKE YI WA KACHAKO
Anayi wa kachako kirari da cewa:
“Kacha-kacha ta Malam Buba, Ta Buba Gaxa da kwari, shiga
da kaya fita da gammo, kachakawa sun taimake ni”.
Dalilin wannan kirari shi ne kachako gari ne na kasuwanci,
kuma yana da babbar kasuwa da take ci ranar Lahadi, kuma tana cike da baqi da
suke zuwa daga garuruwa da ban da ban, kuma duk kayan da ka shigo da shi
kasuwar kachako za a siyar da shi, da sauri sai dai mutum ya koma da gammon sa.
Wannan shi ne dalilin da yasa ake cewa fita da gammo.
SUNAYEN TSOFAFFIN RIJIYOYI NA GARIN KACHAKO
A kwai tsofaffin rijiyoyi a sassa da ban da ban na garin
kachako waxanda suke nuna tarihi, da daxewar kafuwar garin na Kachako, kaxan
daga ciki, su ne kamar haka:
1. Duguruwa
2. Uwar Gwandai
3. Ragi
4. Kwanjava
5. Zariya
6.
Ta-Allah
7.
Loya
8.
Ci fulani
9.
Gwanto
10.
Mamursa
11.
Makama
12.
Madangana
13.
Sha bindiga
14.
Ungulu
15.
Maza tsaye
16.
Ta fare
17.
Dan ta katse da kuma
18.
Lemo
DUGURUWA
Duguruwa tana daga cikin tsofaffin rijiyoyi da masana
suke cewa: “Duguru suma fulani ne da suka sauka a dai dai gurin da rijiyar take
tare da shanunsu, kuma rijiya ce mai tsohon tarihi mai daddaxan ruwa, mai kogo
an ce kogonta ta qasa yana da nisa, kuma wai kogon ta yana haxuwa da wasu
rijiyoyi masu tsohon tarihi irinta kamar Ragi da Kwanjava da sauransu.
TA-ALLAH
An ce daga cikin shanun Jauro Buba Fange akwai wani
bijimi wanda yake fita daga cikin garke, sai ya shiga Daji a guje, sai bayan
wani lokaci aga ya dawo, kuma idan aka zo ba su ruwa sai aga ya qi sha, wata
rana sai aka bi shi, sai aka samu yaje wani guri a cikin Daji ya karta qafarsa
sai ya sa baki ya ci gaba da shan ruwa, yayin da suka duba sai suka ga ashe
rijiya ce a wannan gurin amma ba’asan wanda ya tona ta ba. Wannan ne ya sanya
ake kiranta da Ta-Allah.
KACHAKO A GIDAN SARAUTAR KANO
A cikin wani littafi mai suna “MU SAN KANMU WALI SULAIMAN
A TARIHIN KANO” na Alqali Hussaini Ahmad Sufi (Shafi na 180) ya ce babbar Matar
Sarkin Kano Abbas ana kiranta UWAR GIDA ko FULANIN KACHAKO kuma a
kwai unguwa musamman a gidan Mai Martaba Sarkin Kano da ake kiranta da Kachako.
RUFEWA
A nan zan dakata da wannan xan taqaitaccen tarihi na
garin Kachako, ina fatan ‘Yan Bokonmu da sauran jama’ar mu za su xora domin
samun tabbataccen ko cikakken tarihin garin kachako saboda matasanmu da kuma
yaranmu masu tasowa su san tarihin magabata.
A qarshe ina so nayi amfani da wannan dama domin in
tunawa mai girma Dagacin Kachako na yanzu wanda muka taru anan saboda shi wato ALH.
YUNUSA IBRAHIM cewa: “Kafin rasuwar Dagachin Kachako Bashar Isma’il ya yi
wasu naxe – naxe domin kyautata masarautar kachako, amma kafin a yi bikin
qaddamarwa sai Allah ya yi masa rasuwa” shi kuma mai girma dagacin Kachako da
ya zo bai ce komai a kan waxannan naxe- naxe ba, muna fatan Mai Girma Dagacin
Kachako zai tabbatar da waxannan naxe- naxe, tare da amincewar mai girma
Hakimin Takai Xan Lawan Xin Kano ALH. BASHAR A. DR. ADO BAYERO. Kuma ina godiya da
wannan nauyi da aka xora mini na karanta tarihin Kachako, da fatan za’ayi
haquri da abin da aka ji.
Na gode.
(DR.) YAKUBU MAI GIDA KACHAKO
-
Shatiman Kachako
-
Jarman Daho
-
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano
Phone:
08036420792
Mail: dr.kachako@gmail.com
Web: www.drmaigidakachako.blogspot.com
Subscribe to:
Posts (Atom)