GABATAR DA TAKARDA MAI TAKEN:
ILLOLIN
KIWON KARE A TSAKANIN AL’UMMA
DAGA:
(DR.)
YAKUBU MAIGIDA KACHAKO
MUKADDASHIN
BABBAN KWAMANDAN HISBAH NA
JIHAR
KANO MAI KULA DA AYYUKAN YAU DA KULLUM
RANA: Alhamis 14th Feb. 2013
GURI: Freedom Radio Kano
LOKACI: 5:00 – 6:00 Na Yamma
1434AH/2013
ILLOLIN KIWON A TSAKANIN KARE AL’UMMA
Ma’anar Kare:
الكب
Kuma ana kira wanan
kalma suna cutar Karen.
Wata irin halitta ce ta Allah mai kafafu
(4) da dogon bindi yana kuma da dogon harshe mai lallage, yana kasancewa a
launi mabambanci, wani baki wani ja, d.s. kuma yana da dogayen kunnuwa
mabambanta a tsakanin karnuka na kasashe daban-daban.
Karnuka suna da sunaye kamar Bare, Durwa,
Duna, D.S. kuma kare yana daga cikin Dabbobi masu biyayya da Basira da koyon
abin da aka koya masa a cikin sauri.
Allah ubangiji madaukakin sarki ya buga
misali da kare a wajen lallage da Harshensa a cikin suratul – A’a’raf aya ta
(175-176)
ﭧ ﭨ ﭷ ﭸ ﭹ
ﭺ ﭻ ﭽ ﮩ ﮪ ﮫ
ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ
ﮱ ﯓﯔ ﯕ
ﯖ ﯗ ﯘ
ﯙ ﯚ ﯛ
ﯜ ﯝ ﯞﯟ ﯠ ﯡ
ﯢ ﯣ ﯤ
ﯥﯦ ﯧ
ﯨ ﯩ ﯪ
ﯫ ﭼ الأعراف: ١٧٦
Ma’anar ayar: -
….“…. karanta masu labarin wanda muka
kawo masa (3) ayoyinmu sai ya savule daga gare su, sai shaixan ya bi shi sai ya
kasance a cikin halaka (176) kuma da mun so, da mun xaukaka shi da su, kuma amma
shi ya nemi dawwama a cikin qasa, kuma ya bi son zuciyarsa , to misalinsa kamar
misalin kare ne, idan ka yi dauki a kansa ya yi lallage ko kuwa ka bar shi, ya
yi lallage……”
Dan haka lallage xabi’ace ta kare
Abin tambayarmu anan shi ne: - shin kare
yana yada cutuka a tsakanin al’umma?
Dangane da amsar wannan tambaya ne muka
so mu kawo bayanan malamai da irin mabambanta ra’ayoyin da ke tsakaninsu.
Malam Yusuf Alh Ahmad ya yi babi guda
akan wannan matsala a cikin
littafinsa mai suna:
موسوعة الاعجاز العلمي في القرءا والسنة المطهرة ص (602)
Farko ya fara kawo Hadisin Annabi
[s.a.w.] wanda Imamu Muslim ya kawo daga Abuhuraira cewa:-
"وعن
ابي هر يرة رضي الله عنه قال:- قال رسول الله صلي الله عليه وسلم:- "طهور
اناء احدكم اذا ولغ فيه الكلب ان يغسله سبع مرات اولا هن بالتراب"
“ Manzan Allah [s.a.w] y ace: -
“Tsarkin Kwayar kowannenku idan kare ya
sa baki a cikinta, shine ya wanke ta sau (7) xaya daga cikin wankin ya zama da
Qasa.”
Haka kuma a wani Hadithi da aka karbo daga Ibni Mugaffal, ya ce:
{Manzan Allah (S.A.W) ya ba da umarnin
kashe Karnuka kuma sannan ya ce: me
ye rowanku da Kare,
Haka
kuma Annabi (s.a.w.) ya yi rangwame akan KAREN FARAUTA DA KAREN GADIN DABBOBI,
sai ya ci gaba da cewa: idan kare ya sa baki a kwaryar xayanku, to ya wanke sau
Bakwai xaya daga cikin wankewar ya zamo da
Qasa
Malamai
sun karawa juna sani dangane da ma’anar wannan Hadithin Musmman Kalmar: - اذا ولغ الكلب
Malam Ali Bassam a
cikin:-
توضيحالاحكا م شرح العمدة الاحكا م
Yace : -
A cikin Bakin kare musamman yawunsa
akawai Najasa, dan haka idan har ya sa baki a kwaryar sai an wanke sau (7) xaya
da Qasa
Imamus-Shafi’I ya ce: -
Komai na jikin kare ma Najasa ne don
haka duk abin da ya shiga cikin Qwaryar daga sassan jikin kare, to sai anwanke
sau (7) kamar yadda aka faxa
Amma shi Imamu Malik y ace: -
Babu wata najasa a jikin kare, ko
wankewa ma da aka ce a yisau (7) to ibada ce kawai
Amma wani malami da ake kiransa Dayyyara
a cikin littafinsa mai suna: -
Ya ce: -
“Binciken masna ya tabbatar da cewa shi
kare yana dauke da wata guba a tare das hi y ace wasu tsutsotsi ne ke fita daga
bakinsa masu cutar dad an-Adam
Amma shi mai littafin:
M. Yusuf A. Ahmad cewa ya yi: -
“Ba shakka binciken masana kimiyya ya
tabbatar da cewa kare yana daga cikin Dabbobi masu yada cutuka masu hadari
domin akawai wata tsutsa da take rayuwa a cikin uwar Hanjinsa, ana kiran wannan
Tsutsa da (AL-MAKURAT)
Kwayoyin wannan tsutsa suna fita a cikin
kashinsa, don haka idan kare ya lashi duburarsa da harshensa sai ya kwaso
wannan kwayoyi zuwa kwarya ko kwanon abincin day a sansana ko kuma kwayoyin su
tafi I zuwa hannun wanda duk yake muamala das hi kuma nan da nan wadannan
kwayoyi cuta su kana shiga cikin uwar hanjin Dan-Adam.
Da zarar kwayoyin sun shiga uwar hanji
ko hanji sa su kyankyashe sai jariran tsutsotsi su shiga ko ina a jikin
Dan-Adam ta hanyar jinni musamman cikin hamtar Dan Adam
Irin wadannan tsutsotsi sukan taru guri
guda a sassan jiki su samar da wata jaka matara runga tar ashen lafiya a sassan
jiki ana kiran wannan jaka da: -
Haka kuma irin wanan cutar tanada
hadarin gaske a jiki musamman idan cutar ta kama kwakwalwa ko sassan zuciya ko
wata gaba ta jiki sau da dama idan wannan cuta ta kama jiki sai an yi tiyata.
Haka kuma matsala ta biyu ta kare da
yake yadawa, ga Al-umma it ace: - a cutar kare mai haddasa zazzabi wacce yake
yadawa ta hanyar yawunsa ta hanyar lasa kuma nan da nan wannan cuta ta ke
haduwa a tsakanin Al-umma.
To sai dai kuma ita wannan cuta ta biyu
da ake dauka daga yawun kare malamai masu bincike sun gano cewa: -
“Ba kowane kare ne yake dauke da wannan
cuta ba, Karen da yake dauke da wannan cuta shi ake kira da
Ma’ana: - masifaffen kare ko kare mai
yawan cin kare ko kare mai yawan kai farmaki da sauransu.
WANKE KWARYA SAU BAKWAI DAYA DAGA CIKI
YA ZAMA DA KASA
Akwai maganganun malamai da dama a kan
wannan mas’ala ta wanke kwaryar da kare ya sansana da ruwa da kasa.
-
Wasu suna garin
yin hakan wajibine? Ko kuwa don kyautata tsaftace
-
ALI BASSAM mai y
ace: -
Wasu
malamai suma ganin cewa sanya kasa a cikin wanki bakwai da za’ayi wa kwaryar da
kare ya sawa baki kawai ibada ce, wato bin umarnin manzon Allah ne (S.A.W)
Wannan
kuma shine ra’ayin Imamu MALIK.
Amma
shi malam Ahmad Mursiy Usani Jauhar a cikin littafinsa: cewa ya yi: -
Sanya
kasa a cikin wanke kwarya sau Bakwai hikima ce
ta futar da Datti, domin da can
larabawa ba su da sabulu shi ya sa Annabi S.A.W ya ce: a yi amfani da kasa amma
a yanzu za’a iya amfani da sabulu ko makamancinsa, kuma su tsaya a matsayin
kasar da aka ambata.
Haka
kuma shi Khadimussunna mai littafin cewa yayi: -
Kare
ya na daga cikin Dabbobin da suke yada cuta a tsakanin al,umma kuma bincikde ya
nuna cewa: akwai cutuka da ba su gaza guda (50) ba wadanda ake samunsu a jikin
kare, musamman a yawunsa ko a Duburarsa, kuma wadannan cutuka babu wani sinadari
da yake iya konesu da gareje inba kasa ba.
Malamin
ya ci gaba da cewa: - akwai wata Jami’a ta Amerika da take a kasar Labanoon,
sun gudanar da wani bincike a kan: -
Tasirin kasar makabartu, a kan gawawwakin mutane
wadanda suke mutuwa a sabanin cutuka masu hadari iri daban – daban wasu
kanjamau, wasu teebee, wasu tinjere da sauransu.
In
banda kasa tana kone irin wadannan cutukan da ake mutu das u, to da tasirin su
ya dinga cutar da Rayayyu, saboda haka, hikimar Annabi S.A.W wajen a wanke
kwaryar da kare ya taba daya ya zamo da kasa, ba maganceta tsafta kawaiba domin
kwayoyin cutar da ke fita daga bakin kare zuwa kwayar day a sansana, ba abin da
yake iya kone su da garaje in ba kasaba.
BAMBANCIN
KARE DA KYANWA A WAJEN YADA CUTA:
Bisa
ga bayannan da suka gabata mun fahimci cewa, kare yana yada cutuka a tsakanin
Jama’a musamman ta yawunsa da abin da ke futa daga Duburarsa.
Ita
kuwa kyanwa, an tambayi Annabi (S.A.W) akanta sai y ace: -
Ma’ana:
Ita
kyanwa ba najasa ba ce, kadai dai ita tana daga cikin Dabbpobi masu kaiwa da
komowa a cikinku.
Kuma
ya kasance yana yin al-wala da guntun rowan da tasha ta rage.
Haka
kuma ita kyanwa a wuri daya ne binciken masana kimiyya ta gano cewa: - akwai
wasu kwayoyin cuta da suke cikin kashinta wadanda suke shiga jikin mutum suna
makantar da shi.
Ke nan wannan Daliline yasa Allah (S.W.T) ya
koyar da ita/ya shiryar da ita, idan za ta yi kashi, sai ta tona rami, in ta gama
kuma ta bunne, wannan ko shakka babu hikima ce daga Allah ubangiji madaukakin
sarki.
SHIN
ALJANU SUNA ZAMA KARNUKA HAR SU CUTAR DA DAN-ADAM?
Tabbas
dalili na shari’a sun tabbatar da cewa, akwai Aljanu masu zama karnuka, ko kuma
masu Nau’I irin Nau’in karnuka.
Hadisi
ya tabbat riwayar Dabrane da Hakim da Baihakiy da Samadi ingantacce, manzon
Allah (S.A.W) y ace: -
Ma’ana:
-
“Aljanu
Nau’I uku ne: -
-
Akwai nau’in da
suke da Fukafukan da suke tashi sama da su,
-
Da nau’in da
suke kamar macizai da karnuka,
-
Da kuma masu
zama a wani bugire sukuma ta shi su yi gaba wani lokaci.