GABATAR DA JAWABI AKAN MATAKAN KIWON LAFIYA A
MUSLUNCI
MAI GATARWA:-
{DR.} YAKUBU MAIGIDA KACHAKO
DCG/OPS
KANO STATE HISBAH
RANA:- ASABAR 8/9/1435 AH=5/7/2014
WURIN TARO:-
MAKARANTAR ALIYA KANO.
LOKACI:- 10:00 NA SAFE
2014
GABATARWA
Haqiqa an gaiyyace
ni domin na gabatar da bayani akan MATAKAN KIWON LAFIYA A MUSLUNCI kuma an haxa
ni da Malamina a matsayin shugaban zama, ko-da-yake ba a sanar da ni vangaren da
ake so a kalla ba a kiwon lafiyar to,
sai de na zava wa kai na in xauki kiwon lafiya a matakin halittar Xan-adam.
Ina roqon Allah ya ba ni ikon
gabatar da wannan bayani cikin nasara.
Ba shakka Allah shi ya halicci Dan-Adam
kuma ya fifita shi akan sauran halittu da abubuwa guda huxu:-
1.
Kirar jiki,
2.
Hankali,
3.
Ilimi, da kuma
4.
Shari’a
Ita kuwa shari’a an kawo ta ne domin ta kare wa dan-adam hakkoki guda
biyar, su ne:-
1.
Hakkin Addini
2.
Mutunci,
3.
Dukiya
4.
Nasaba. da kuma
5.
Hakkin Rai,
Wanda a qarqashinsa
ne maganar kula da lafiya ta shigo.
Akwai girmamawa a cikin hlittar Mutum a cikin Mahaifa, da yadda ya tsara
masa
Nakuda da haihuwa, shayarwa, da
kuma rainon abin da aka haifa, da ba shi
Tarbiyya.
SHIMFIXA
Ko shakka babu
musulinci ya bayar da da cikakkiyar kulawa game da sha a nin kiwon lafiya, har
ma masu iya Magana suna cewa:-
“Wato –Dirhami daya na riga kafi; ya fi Dirhamin neman magani alkhairi.”
Musulunci shi ne
wanda ya fara sanya tubalin farko dangane da kiwon lafiya, a bi sa tsarin
koyarwar manzon Allah [s.a.w]. Kamar yadda musulunci shi ne Addinin daya-xaya wanda
ya zo da tsari tabbatacce wanda ya tsara cikin likitanci da kiwon lafiyar, Al’umma,
kwatankwacin abinda ake kira a zamanin nan namu.
Imamu Tirmizii ya fitar da Hadisin Abu Hurayra, daga Annaabi [s.a.w] ya
ce:-
“Farkon abin da za
afara tambayar Bawa akansa na ni imomi a ranar al’kiyama,
shi ne:- “shin ban inganta maka lafiyar jikinka ba? Na kuma shayar da
kai daga ruwa mai sanyi”?....
An samo daga Al-imamu shafa’I, Allah yayi masa rahama yana cewa----
“ Ilimi ya kasu kashi biyu:-
1. Ilimin Addini da za a Bauta wa
Allah ta’ala. da
2. Ilimin da za a kula da kiwon lafiytar jiki.
MA’ANAR KALMAR
LAFIYA.
Malamai sun ba wa wannan kalma fassar iri-iri misali:-
1.
Kuvutar da jikin xan-adam daga kamuwa daga
kocce irin cuta.
2.
Warkewa daga cuta jiki ya sami lafia.
MA’ANAR KIWON LAFIYA
Lafiya shine halin da dan-adam ke samun kansa na jin daxi ba tare da ya
ci karo da kowacce irin cuta ko rashin lafiya ba, ya zama wajibi lafiya ta
kasance abisa waxannan matakai kamar haka—
I.
Lafiyayyen jiki
II.
Lafiyayyen hankali
III.
Lafiyayyun abokan zama
Ko shakka babu lafiya
tana daga ma fi girman Ni’imomi da Allah
ya yi
wa Dan- adam. Domin rayuwa ta arzuki tana da alaqa da kiwon lafiya.
Saboda

Saboda MU KWANA A NAN.