GABATAR DA TAKARDA MAI TAKEN
SIRRIN HANA YAWAN MaCE-MACEN AURE.
RANA:-ASABAR (13/12/2014)
LOKACI:-4:00 NA YAMMA
GURI:NASIRIYYA PRIMARY SCHOOL KWALABE KANO
A YAYIN BIKIN AUREN HAJARA ADAMU HOTORO KANO
2014=1436 A.H
GABATAARW
Allah Ta'ala Ya ce:
فانكحوا
ما طاب لكم من النساء مثني وثلاث ورباءفان خفتم ان لا تعدلوافواحدة.....
النساء: ٣
Ma’ana: "Ku auri abin da ya yi muku dadi daga mataye kobiyu, ko uku, ko hudu".
Sannan ya tabbata a sunnar Annabi (SAW) ya ce:-
"تزوّجوا الودود الولود،
فإنّي مكاثر بكم الأمم يوم القيامة
رواه
أحمد
Ma'ana: "Ku yi aure na soyayya don ku hayayyafa, domin zan yi
bugun-gaba da yawan al'umma a ranar alkiyama”.
ZABAR MUJI
Shara'ar Musulunci ta koyar da yadda akeZabar Muji.
Dangane da fadin Manzon Allah (S.A.W).
"إذا أتاكم من ترضون خلقه
ودينه فزوّجوه إلاّ تفعلوا تكن فتنة في الأرض وفساد كبير
رواه
الترمذي وقال فيه حسن غريب.
Ma'ana: "Idan wanda kuka yarda da Halayensa da Addininsa ya zo neman
Diyarku, to ku aura masa, inba ku yi
hakan ba, fitina za ta faru a bayan kasa da barrna mai girma.
§SIFFOFIN MIJI NA GARI
•Mai Addini.
•Mai Ilimi.
•Mai Sana’a.
•Dan Dattawa.
•Mai iya mu’amala.
•Mai Tsabta.
•Mai Tausayi.
•Mai gaskiya da Amana.
•Mai cika alkawari.
•Mai iya soyayya.
•Mai rike sirri.
•NEMAN AURE
•1. Bin ka’idojin Addini yayin nema..
•2. Kada a kula juna
•3. kada a yi wa juna karya,
•4. Kada a yi dogon buri.
•5. Banda yaudara
•Ds.
§TARIYA:
§Akwai laduba da yakamata ma'aurata su
sifantu da su.
An so idan ango zai shiga wajen amaryarsa ya yi abubuwa kamar haka:
Magana mai taushi,
Gabatar da wani abin ci ko sha.
Kamar yadda ya tabbata Manzon Allah
(S.A.W) ya yi lokacin da zai tare da matarsa Assaiyida Aisha; sai ya shigada Nono a wani koko.
1.Magana mai taushi,
2..Gabatar da wani
abin ci ko sha.
3.SALLAH
§An so Ango da Amarya su yi sallah ta nafila raka'a biyu a tare, domin an
samu magabata na aiwatar da haka, kamar Asar din Abi Sa'idin Maula abi Asyad ya
ce:
"Na yi Aure ina Bawa, sai na gayyaci wani kaso na sahabban Annabi
(SAW) a cikinsu akwai dan Mas'ud da Abu Zarin, sai ya yi nufin ya wuce, amma
sai suka umarce ni da na wuce a matsayi na na Bawa,
Suka kuma koyar da ni cewa:
Dora hannu a goshin Amarya da yimata addu'a:
Saboda Hadisin da ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) cewa:
"إذا تزوج أحدكم امرأة، أو اشترى خادمًا،
فليأخذ بنا ميتها، وليسم الله عزّ وجل، وليدع بالبركة، وليقل: "اللهم إنـّي
أسألك من خيرها وخير ما جبلتها عليه، وأعوذ بك من شرها وشرما جبلتها عليه.
SADUWA:
1.Yin Addu'a – Saboda hadisin Bukhari:
2."بسم الله، اللهم جنّبنا
الشيطان، وجنب الشيطان ما رزقتنا"
GABATAR DA JAWABI AKAN MATAKAN KIWON LAFIYA A
MUSLUNCI
MAI GATARWA:-
{DR.} YAKUBU MAIGIDA KACHAKO
DCG/OPS
KANO STATE HISBAH
RANA:- ASABAR 8/9/1435 AH=5/7/2014
WURIN TARO:-
MAKARANTAR ALIYA KANO.
LOKACI:- 10:00 NA SAFE
2014
GABATARWA
Haqiqa an gaiyyace
ni domin na gabatar da bayani akan MATAKAN KIWON LAFIYA A MUSLUNCI kuma an haxa
ni da Malamina a matsayin shugaban zama, ko-da-yake ba a sanar da ni vangaren da
ake so a kalla ba a kiwon lafiyar to,
sai de na zava wa kai na in xauki kiwon lafiya a matakin halittar Xan-adam.
Ina roqon Allah ya ba ni ikon
gabatar da wannan bayani cikin nasara.
Ba shakka Allah shi ya halicci Dan-Adam
kuma ya fifita shi akan sauran halittu da abubuwa guda huxu:-
1.Kirar jiki,
2.Hankali,
3.Ilimi, da kuma
4.Shari’a
Ita kuwa shari’a an kawo ta ne domin ta kare wa dan-adam hakkoki guda
biyar, su ne:-
1.Hakkin Addini
2.Mutunci,
3.Dukiya
4.Nasaba. da kuma
5.Hakkin Rai,
Wanda a qarqashinsa
ne maganar kula da lafiya ta shigo.
Akwai girmamawa a cikin hlittar Mutum a cikin Mahaifa, da yadda ya tsara
masa
Nakuda da haihuwa, shayarwa, da
kuma rainon abin da aka haifa, da ba shi
Tarbiyya.
SHIMFIXA
Ko shakka babu
musulinci ya bayar da da cikakkiyar kulawa game da sha a nin kiwon lafiya, har
ma masu iya Magana suna cewa:-
“Wato –Dirhami daya na riga kafi; ya fi Dirhamin neman magani alkhairi.”
Musulunci shi ne
wanda ya fara sanya tubalin farko dangane da kiwon lafiya, a bi sa tsarin
koyarwar manzon Allah [s.a.w]. Kamar yadda musulunci shi ne Addinin daya-xaya wanda
ya zo da tsari tabbatacce wanda ya tsara cikin likitanci da kiwon lafiyar, Al’umma,
kwatankwacin abinda ake kira a zamanin nan namu.
Imamu Tirmizii ya fitar da Hadisin Abu Hurayra, daga Annaabi [s.a.w] ya
ce:-
“Farkon abin da za
afara tambayar Bawa akansa na ni imomi a ranar al’kiyama,
shi ne:- “shin ban inganta maka lafiyar jikinka ba? Na kuma shayar da
kai daga ruwa mai sanyi”?....
An samo daga Al-imamu shafa’I, Allah yayi masa rahama yana cewa----
“ Ilimi ya kasu kashi biyu:-
1. Ilimin Addini da za a Bauta wa
Allah ta’ala. da
2. Ilimin da za a kula da kiwon lafiytar jiki.
MA’ANAR KALMAR
LAFIYA.
Malamai sun ba wa wannan kalma fassar iri-iri misali:-
1. Kuvutar da jikin xan-adam daga kamuwa daga
kocce irin cuta.
2. Warkewa daga cuta jiki ya sami lafia.
MA’ANAR KIWON LAFIYA
Lafiya shine halin da dan-adam ke samun kansa na jin daxi ba tare da ya
ci karo da kowacce irin cuta ko rashin lafiya ba, ya zama wajibi lafiya ta
kasance abisa waxannan matakai kamar haka—
I.Lafiyayyen jiki
II.Lafiyayyen hankali
III.Lafiyayyun abokan zama
Ko shakka babu lafiya
tana daga ma fi girman Ni’imomi da Allah
ya yi
wa Dan- adam. Domin rayuwa ta arzuki tana da alaqa da kiwon lafiya.
Saboda

Saboda MU KWANA A NAN.