GABATAR DA TAKARDA MAI TAKEN
KAYAN
SA MAYE NA GARGAJIYA,
DA
ILLOLIN
RANA:- 13/4/2013
GURI:- AFIRKA HOUSE
LOKACI:- 10:OOAM
SHIRYAWA DA XAUKAR NAUYI:-
{CWYI} CARE WOMEN AND YOUTH INITIATIVE
MAI GABATARWA:- {DR.}
YAKUBU MAIGIDA KACHAKO
DCG/OPS HISBAH KAN
1434AH=201
GABATARWA
Ba shakka
al’amarin amfani da kayan sa maye ya zama rowan dare gama duniya, domin babu
wata Nahiya da ba a shaye-shaye, sai de a sami bambance-bambance saboda yanayin
wayewa, ko tattalin arzuqi, ko kuma kokarin shugabannin wannan
Nahiya wajen daqile harkar shaye-shaye.
Wannan gangami da wannan qungiya take shiryawa a
qarqashin jagorancin Maigirma Matar Mai girma Mataimakin Shugaban Qasa, ya zo
dai-dai da lokacin Al’ummar Nageriya ke buqatarsa. Sanna yayi dai-dai da
yunqurin gwamnatin jahar kano na yaqi da kaya sa Maye, a aikace.
Abubuwa uku ake gudu game da Illar shaye-shaye, su
ne:-
1.
Shigar Mata
harkar shaye-shaye,
2.
Shigar qananan
Yara. Da
3.
Shigar Matasa
harkar shaye-shaye.
Ø Illar
shaye-shaye a gurin Mata ita ce:- “Rushewar Tarbiyya” saboda su ke xaukar ciki, shayarwa, reno da
Tarbiyya in suka zama ‘yammaye akwi Matsa….
Ø Yara
daga primary, zuwa Sakandare, idan suna
shaye-shaye, da wuya suke iya dainawa,
ko da sun tafi Jami’o’i, kuma su a ke sa ran su zama shugabanni nan gaba, ko
kuma su zama Jami’an tsaro, to, kuwa idan ya zama tsaron lafiya da dukiyar masu
hankali, ya koma hannun Yara ko Matasan da ke shaye-shaye, masu rushasshen
hankali, to, ba shakka a kwai tashin hankali, Allah ya kiyaye amen.
Danhak mu muna goyon bayan irin wannan yunquri a
matakai da ban da ban,kuma matakan da gwamnatin jahar kano take xauka na sama
wa Matasa aiyyukan yi, ko shakka babu, zai magance shaye-shaye.
Sai de kawai a ci gaba da jajircewa domin yaqi da
kayan sa maye, a gurin masu sha da sayarwa, kamar masu wankin gyanbo ne da mai
gyanbo, kullum mai gyanbo bay a gane sonsa a ke sai bayan ya warke, haka mai
shan kayan maye da mai sayarwa suke.
TARIHIN KAYAN SA MAYE A DUNIYA:
Ba a samu wani takamaiman gamsasasshen
bayani ba, da yake nuna asalin faruwar xabi'ar shaye-shayen miyagun qwayoyi ko
amfni da kayan sa maye ba.
Qoqarin neman magani da jarrabawa, ya
fara ne tun lokacin da xan Adam ya fara rayuwa, rayuwar xan Adam ita ce faruwar
amfani da magani, domin tun zamani mai tsawo lokacin da xan Adam ya fara
rayuwa, an samu yana sarrafa itatuwa da tsirrai domin magance cutukan da suka
dame shi, daga cikin itatuwan da yake sarrafawa, har ya samo waxanda za su
gusar da hankalinsa, ko su sa shi farin ciki, ko su qara masa qarfin jiki, ko
kuma ya yi amfani da su, domin abin da ya shafi sihiri.
Ana cikin wannan rayuwa ne, malamai suka
ci gaba da bincike domin tantance irin waxancan itatuwa da tsirrai, har suka
kai ga ware masu sa maye da masu kashe zafin ciwo da raxaxi, da masu sa barci,
da waxanda ke rage zafin damuwa da xan Adam ke samun kansa a ciki. Wannan ne ya
jawo aka dinga shuka irin waxannan tsirrai, da kuma samar da cibiyoyin sarrafa
su, aka dinga daidaita wasu masu tsanani daga cikinsu domin su dace da jikin
xan Adam, to, waxannan su ake kira kayan sa maye, waxanda aka samo asalinsu
daga tsirrai, da maganin gargajiya, kamar:-
WIWI(GANYE),
OPIYON, KOKEN, da sauransu.
Daga
waxancan sarrafe-sarrafe ne duniyar kimiyya ta samar da sababbin kayan sa maye,
ta hanyar: QWAYOYI, "KAFSO, WAXANDA AKE SHAKAWA TA HANCI, KO KUMA SHA TA
BAKI" kuma dukkansu suna da illoli iri xaya da wanda waxancan na tsirran
ke da su.
Akwai savanin malamai dangane da
iyakance tarihin kayan maye a Duniya, yaushe ne a ka san su? Yaushe aka fara
amfani da su? Ta yaya suka yaxu a Duniya? Sannan abin da ya fi bayyana ita ce
tabar wiwi, domin ita ce kan gaba da xan Adam ya fara sani kafin ya san sauran
kayan maye.
Break A'idul Karni a cikin littafinsa المخدرات الخطر
الإجتماعي الداهم""
ya
ce:
"Ana qaddara asalin samuwar kayan
sa maye, tun shekaru (5,000) kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) kuma an fara samun
sa ne a vangaren Asiya ta kudu da gabacin kogin (البحر الأبيض المتوسط) wato "White Middle
Sea".
"Mutane,
ba su fahimci (KOKEN DA OPIYON" waxanda ake samunsu daga tsirrai da
itatuwan gargajiya ba, sai a farko-farkon qarni na (20). Lokacin da wani
mutumin qasar "GERMANY" da wasu mutane biyu na qasar
"FARANSA" suka qirqiro wani magani mai sa nishaxi daga (OPIYON) kuma
shi mutumin (JAMUS) xin shi ya sa masa suna (SIRATORINO) daga sunan marofin,
mai dangantaka da marofis, a yaren (GIRKAWA) kuwa: Kalmar tana nufin (NA'URAR
TUNANI). An ci gaba da amfani da marofin a matsayin magani mai sanya nishaxi ga
jiki, har zuwa shekarar (1861-1875) lokacin da aka yi yaqin cikin gida na
Amirka, (American Civil War) aka gabatar da marofin ga sojojin Amerika
domin ya sauqaqa masu zafin raunin da suka samu a wannan yaqin, daga nan su
kuma sai suka yawaita amfani da shi, har ya zama kayan sa maye a gare su.
Haka kuma sojojin Rasha da suka yaqi
Faransa a shekara ta (1870) da kuma sojojin da suka yi yaqin Duniya na farko
(1912-1918) a cikinsu an sami adadi mai yawa na mashaya marofin a qasashen
America da Turai(1).
Haka kuma a shekara ta (1889) wasu
malamai na qasar (INGILA) suka samar da sabon bincike a kan wancan magani na
(MAROFIN) wanda ya samar da adadi mai yawa na masu maye daga sojojin Amirika da
Turai, suka kira sunan binciken nasu da (DAY-ISTIL-MOROFIN) aikinsa yi wa masu
shan (OPIYON DA MOROFIN) magani, a wajen sayarwa sai ake kiran sa da (HIROYIN)
a inda aka dinga fitar da shi a matsayin magani, har zuwa shekara ta (1898) a
inda aka kafa Kamfani na musamman mai suna (BAYAR ALMANIYA).
A farkon fitowarsa ana amfani da shi ne,
don warware matsalar mashaya (Morfin da Opiyon) kamar yadda aka faxa a baya, har
malaman qasarsu suke ganin kamar maganin ba shi da wata illa, amma daga baya
sai 'yan fashi da waxansunsu, suka gano ya fi kowanne kayan sa maye amfani a
gunsu.
Yaxuwar Hiroyin "HEROIN" a
duniya ya samo asali ne daga sojojin (INGILA) da (JAPAN) kuma su ke qarfafa
guiwa wajen sayar da ita da kuma fataucinta, har zuwa lokacin da aka yi yaqin
Duniya na biyu.
Haka kuma, qasashen AMERICA da MISRA, da
CHINA, sun taimakawa wajen sayar da (HIROYIN) a inda China ta zama wata cibiya
wajen samar da ita.
Amma
dangane da Hodar Iblis (Koken) Duniya ta gano tasirinta wajan sa maye ne a
shekara ta (1876) sai dai ita ma a farkon samar da ita, an yi ta ne domin
magance rauni. Ba'a gurvata hanyar amfani da (Koken) ba sai a shekara ta (1890)
lokacin da (PERU) suka kafa kamfanin samar da ita, da fitar da ita zuwa
qasashen waje, Hakan ta faru ne a tsakanin baqaqen fata mazauna qasar
(Amirika). Daga nan sai mawaqa da masu harkar funa-funai, suka xauki Hodar
iblis/Koken a matsayin kayan sa maye.
Amma
dangane da (GANYE) kuwa wato (TABAR WIWI) wadda a yanzu 'yan zamani musamman
matasa, suke yawan amfani da ita, kuma suke ba ta sunaye iri-iri kamar:-
-
Karas.
-
Marijuwana.
-
Bahanij.
-
Kaifu,
-
Daja.
-
'Yarmo.
-
Indian – hemp
-
Ganye.
-
Kaya.
-
Igbo
-
Stone
-
Hashis
-
Ganja
-
Grass d.s.
Kusan
kowa ya amince da cewa, ita ta fi kowane kayan maye daxewa a Duniya. Kuma ita
ce aka fi amfani da ita ko'ina cikin duniya.
Ana samun tabar Wiwi ne daga itacen (القنب والتفرز) (Canabis Sativa) a jikin itaciyar taba wiwi,
akwai huda da ganye, kuma da wannan ganyen ne ake yin taba wiwi, a can baya
zamanin magabata, an fi shuka ta a qasar indiya, da manyan qasashen Asiya da
Afrika da kuma America(1).
M. Mustapha Abbasiy a cikin littafinsa
mai suna
(أسرار
المخاطرة التي تنتج عن تدخين السجائر والحشيشه...)
Ya
ce:- "Binciken masana na Duniya ya tabbatar da cewa: "A duk cikin
mutum bakwai na Duniya, za a sami guda mai shan tabar wiwi, ko kuma wanda ya
tava sha"(2).
Tun shekaru (2733) kafin haihuwar Annabi
Isa (A.S) qasar China suka fara bincike a kan taba wiwi, ta hanyar (Akarabazin)
kuma suke amfani da ita, har abin ya watsu izuwa qasashen Misra, da Indiya, da
Greak, da Afrika, da kuma yankin Larabawa.
A qasashen Turai kuwa Faransa ce ta
rungumi xabi'ar amfani da tabar wiwi, saboda sojojin da suka dawo daga yaqin
Barnabat a Misra, su suka zo masu da ita.
An gano tabar wiwi a matsayin xaya daga
cikin kayan sa maye ce tun a qarni na (10) kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) haka
abin ya ci gaba da yaxuwa ta matakai daban-daban a qasashen Duniya.
Amma Girkawa su ne farkon waxanda suka
siffanta tabar wiwi ta hanyar zane, an kira wannan aiki nasu da suna:
(DIYOSOKORIDIS) daga hannunsu ne likitocin larabawa da na Farisa, suka Siffanta
wannan tsiro (Tabar wiwi) har su mutanen Farisa suka yi bincike, suka gano irin
yanayin mayen da tabar wiwi take haddasawa.
KAYAN
SA MAYE NA GARGAJIYA
Su kayan sa maye, sun kasu kashi-kashi,
gwargwadon yadda yanayin jama'a yake da yanayin mazauni, da ilimi, da tarbiyya,
da yanayin tattalin arziqin yankin yake. Amma masana wannan fannin sun raba kayan
sa maye zuwa rukuni-rukuni, kuma daga cikinsu akwai masu sa mayen kai tsaye,
akwai waxanda sai an yi amfani da su fiye da kima, sannan za su sa mayen, a
kwai kuma waxanda xaukar lokaci wajen amfani da su ke sa su dinga sanya maye.
Haka kuma akwai kayan mayen da ke iya
dakatar da harkar jiki, ko ya motsar da ita, akwai kuma masu tasiri ga hankali
da jiki, kamar:-
-
Sanya Buguwa.
-
Sanya ruxewa.
-
Shiga halin matsanancin maye.
-
Sanya matsanancin Barci. Ko sanya
rashin barci.
1. Rukunin
kwayoyi ko magunguna (ILLICET DRUGS).
2. Rukunin
masu tiriri da bin iska (VOLATILE
SUBSTANCES/VOLATAYAL SABTANCES)
-
Rukunin kway Petrolium – (Fetur).
-
Glue – (Gulu)
-
Rubber solution – (Sholisho).
-
Ingine Oil – (injin oyil)
-
Crosene – (Kalanzir)
-
Liquid Paraffin (Lukuy Farafin)
-
Correction Flued – (Korrektin
flu)
-
Sucudine –
3.
Rukunin
sinadarai (CHEMICAL)
-
Dyes.
-
Fartelizer.
-
Mahabbalan.
-
Gishirin lalle.
-
Cocaine – (Hodar Iblis)
-
Canabies/India-hemp/Marijuwana/wiwi/karas/bahanij/Daja/
Kaif/'Yarmo/Ganye d.s.
4. Rukunin
wasu nau'o'i na daban (MISLENIOUS/MISLINIYOS).
- wannan vangare shi ne vangaren
d azan yi jawabi na a kansa, kuma ya
shafi kayan sa maye na daban, waxanda ba su shiga cikin waxancan rukunin ba
kamar:-
ABUBUWAN
GARGAJIYA MASU SANYA MAYE:
Kamar
yadda muka faxa a can baya cewa:-
Kowacce nahiya ta jama'a tana da
hanyoyin da take qiriqrar abubuwan da suke iya jawo maye, ga jama'arta, ko dai
don wayewar da suka samu, ko kuma tsadar rayuwa, ko kuma nisan da suka yi ga
kayan sa maye na zamani, haka su ma al'ummar Hausawa ko kuma al'ummar da ke
zaune a qasar Hausa, suna da dabarun qirqirar kayan mayen da ba za ka sami
irinsa a wata nahiyar ba.
Mashayan qasar Hausa sukan yi amfani da
wasu abubuwa da a zahirinsu ko asalinsu ba kayan sa maye ba ne, amma an canza
su an mai da su kayan sa maye.
Haka kuma kamar yadda larabawan
jahiliyya suke yin amfani da dabino da inibi don yin giya, to haka su ma
maguzawan da ke zaune a wasu vangarori na qasar Hausa suke yin amfani da Dawa
da wasu nau'o'i na hatsi domin yin giya, kuma da irin wannan hatsi ne suke
sarrafa nau'o'in giya iri daban-daban kamar:-
-
Burkutu (Hatsi).
-
Bammi (Ruwan kwakwa)
-
Tsama-tsama (Hatsi) d.s.
GA IRE-IREN ABUBUWAN DA AKE AMFANI DA SU A
MATSAYIN KAYAN SA MAYE A QASAR HAUSA:
1. Kashin
qadangare (farin)
2. 'Ya'yan
Darbejiya.
3. Zaqami/Babba
juji
4. Zurman.
5. Bi-ni-da
zugu.
6. Bula.
7. Lalle
(saiwarsa).
8. Hankufa
(Tana sa tsaurin rai da kuma son yin faxa ita suke bai wa tsuntsu kanari domin
ya yi ta kuka ba tare da gajiya ba).
9. Ruwan
kwata.
10.Icen Kukkuki.
11.Gunar shanu
(tana da xaci kuma tana sa gudawa)
12.Xan-kamaru
(maganin barci)
13.Mur (Yana da
xaci zai iya lalata hanta).
14.Takardar Jarida.
15.Kyankyaso
(kafata).
16.Turirin Masai.
17.Gadagi.
18.Tushiyar dawa
19.Qwaxo (Ruwan
bayansa guba ne wanda maciji ke sha domin samun dafi).
20.Igiyar-kaba.
21.Maganin sauro na
(Hayaqi)
22.Cefane(Haxa
rukunin magunguna).
23.Tsumi (haxa
rukunin kayan maye).
24.Omo.
25.Fiya-fiya.
26.Kananzir.
27.Hoda gas.
28.Tokar Taba.
29.Kan ashana
30.Kashin Jaki.
31.Kashin vera.
32.Sholusho (Ya fi
komai haxari domin kala shida (6) ne, guda biyu (2) ne kawai ake yin faci da
su, amma sauran duk shan su ake, kuma ya
fi sauqin samu(1).
Haka kuma shi
babba juji wato zaqami, an daxe ana amfani da shi a matsayin abu mai sa maye
musamman ma a wuraren bukukuwan Hausawa, har ma sakkwatawa sukan yi masa waqa
yayin da ake biki, misali:-
33."NI
BA NI SHAN BABBA JUJI,
34.SAI
RANDA 'YATA TAH HAIFE,
35.KO
RANDA 'YA TA TAH HAIFE,
36.SAI
NAI HURA IN AZA NONO,
37.IN
XAUKI XAN XA IN GORE,
38.IN
HAUKACE IM BI DAJI".
39.
Waxannan su ne kaxan daga cikin abubuwan
da ake amfani da su a wani vangare na qasar Hausa a matsayin kayan sa maye.
HANYOYIN
MAGANCE SHAYE-SHAYE GA MATASA
Babban burin kowacce qasa ko jiha shi ne
so take ta ga 'yan –qasarta sun zauna lafiya, tare da cikakken hankali da bin
doka, wannan shi zai sa a sami zaman lafiya da ayyukan cigaba a kowacce nahiya.
Haka kuma matasa su ne qashin bayan
cigaban kowacce al'umma idan har sun gyaru, amma idan suka lalace, sun zama
haxarin rayuwar kowacce nahiya, kuma babbar hanyar lalacewar matasa ita ce:-
(Shaye-shaye), idan har matasan gari,
suna shaye-shaye to za a iya samun kowanne irin nau'i na matsala a wannan gari,
kamar:-
-
Rashin bin doka.
-
Aikata miyagun laifuka.
-
Kawo cikas ga ayyukan raya qasa.
-
Rashin Tarbiyya, da kuma
-
Lalacewar Nasaba, ta fuskar
haihuwar 'ya'ya marasa cikakkun iyaye.
Ko
shakka babu ya zama wajibi kowacce qasa ko jiha, ko gari, qauye ne ko birni, ya
tashi tsaye domin nemo hanyoyin magance matsalar shaye-shaye ko amfani da kayan
sa maye, wannan ita ce maslaha, da kuma zaman lafiya. A qarqashin wannan
bincike na yi nazarin wasu hanyoyi da nake ganin idan an bi su, za a magance
wannan mummunar xabi'a, da ta addabi duniyar matasan wannan zamani da muke
ciki.
Hanyoyin ga su kamar haka:-
1-WA'AZI
DAGA MALAMAI:-
Wa'azin malamai wata babbar hanya ce da
za ta taimaka wajen magance matsalar shaye-shayen ga matasa.
2-BAIYANAWA
DA YAYATA HUKUCIN KAYAN SA MAYE A MUSLUNCI.
3-GUDUNMAWAR
IYAYE DA 'YAN UWA:
Iyaye su kula da tarbiyyar 'ya'yansu tun
daga neman Aure, da goyon ciki, da reno ,
da lura da abokansu idan sun fara tasowa
4-GUDUNMAWAR
'YAN UNGUWA:
Mutanen unguwa su dinga kakkafa
kwamitoci domin hana yara sha da sayar da miyagun qwayoyi a unguwa.
5-GUDUNMAWAR
QUNGIYOYIN SA KAI NA KOWAN GARI:
Kowacce qungiya ta fito da wata hikima
ta hana shaye-shaye a gari.
6-ILIMIN
KOYAR DA ILLOLIN KAYAN SA MAYE YA ZAMA CIKIN
TSARIN MANHAJAR KARATUN SAKANDARE
Ya kamata ya zama cikin tsarin manhajar
karatun sakandare, a sanya ilimin sanin illolin kayan sa maye a ciki, yin haka
zai sa a shawo kan
wannan matsala in-Sha-Allahu.
7-SAMAR
DA AYYUKAN YI GA MATASA
Akwai buqatar gwamnati ta samar da
ayyukan yi, ta fuskar kafa masana'antu d.s. masu kuxi, da qungoyoyi, da sauran
vangarorin jama'a, su bai wa gwamnati goyon baya, ta wajen samar da aikin yi ga
matasa da koya musu sana'o'i.
8-KAKKAFA
QANANAN MASANA'ANTU A BIRANE DA QAUYUKA
Wannan zai sa kowanne matashi ya sami
abin yi.
9-BAI
WA HUKUMAR HANA SHA DA FATAUCIN MIYAGUN QWAYOYI (N.D.L.E.A.) HAXIN KAI WAJEN
GUDANAR DA AIKINTA.
Sau da dama idan 'yan wannan hukuma,
suka shiga unguwa ko gari domin kama wani mai laifi 'yan unguwa sukan taru su
hana a tafi da mai laifi, ko su je su yi, belinsa ko su hana hukunta shi, ko
kuma a voye mai laifi a qi nuna shi. ya kamata a daina yin haka.
10-
SHIRYA TARUKAN QARA WA JUNA SANI GA MATASA.
A dinga shirya taron qara wa juna sani,
ga limaman juma'a qungiyoyin xalibai, da na aikin gayya, masu koyar da darasin
Addini a makarantu, da sauran muhimman mutane, su kuma su ci gaba da karantar
da jama'arsu.
11-HUKUNTA
MASU FATAUCI DA SHAN MIYAGUN QWAYOYI DA HUKUNCI MAI TSAURI.
Idan muka duba qasar Saudi Arabiyya tana
zartar da hukuncin kisa ga masu shigar musu da qwaya ko a jikin bizar shiga
qasarsu ana rubutawa valo-valo, cewa duk wanda aka kama
ya shiga da miyagun qwayoyi to, hukucin kisa ne.
12-
QUNGIYOYIN LAFIYA DA MAKARANTUN KIMIYYA DA GWAMNATI, SU DINGA SHIGAR DA MASU
MAGUNGUNAN MUSULUNCI CIKIN SHIRIN HANA SHA DA FATAUCIN MIYAGUN QWAYOYI:
13-
ATSANANTA WAJEN HANA SHIGO DA KAYAN SA MAYE DAGA WAJE.
14-RABA
MATASA DA BANGAR SIYASA.
(1) بريك عائض القرني، المخدرات الخطر الإجتماعي الداهم، ص:26، مجلد، دار ابن
خزيمة سنة (1425-2005)
(1) العباسي، أسرار المخاطر التي تنتج...، مجلد، ص:102، جدة، سنة 2006م.
(2) المصدر السابق، ص:102.
(1) M. Abbas A. Abbas (MNIM) Paper Presentation at
Summit on Youths Drugs and Security 15/April,
2008 at Dutse Jigawa State
Library Complex.
No comments:
Post a Comment