Saturday, 21 June 2014

ILLOLIN KARE GA DAN-ADAM




GABATAR DA TAKARDA MAI TAKEN:

ILLOLIN KIWON KARE A TSAKANIN AL’UMMA
DAGA:

(DR.) YAKUBU MAIGIDA KACHAKO
MUKADDASHIN BABBAN KWAMANDAN HISBAH NA
JIHAR KANO MAI KULA DA AYYUKAN YAU DA KULLUM

RANA:              Alhamis 14th Feb. 2013
GURI:               Freedom Radio Kano
LOKACI:           5:00 – 6:00 Na Yamma
1434AH/2013


ILLOLIN KIWON A TSAKANIN KARE AL’UMMA
Ma’anar Kare:  
                                                                                                 الكب 
Kuma ana kira wanan kalma suna cutar Karen.
Wata irin halitta ce ta Allah mai kafafu (4) da dogon bindi yana kuma da dogon harshe mai lallage, yana kasancewa a launi mabambanci, wani baki wani ja, d.s. kuma yana da dogayen kunnuwa mabambanta a tsakanin karnuka na kasashe daban-daban.
Karnuka suna da sunaye kamar Bare, Durwa, Duna, D.S. kuma kare yana daga cikin Dabbobi masu biyayya da Basira da koyon abin da aka koya masa a cikin sauri.
Allah ubangiji madaukakin sarki ya buga misali da kare a wajen lallage da Harshensa a cikin suratul – A’a’raf aya ta (175-176)                               
ﭧ ﭨ ﭷ ﭸ ﭹ
 ﭺ ﭻ ﭽ                                                                              الأعراف: ١٧٦
Ma’anar ayar: -
….“…. karanta masu labarin wanda muka kawo masa (3) ayoyinmu sai ya savule daga gare su, sai shaixan ya bi shi sai ya kasance a cikin halaka (176) kuma da mun so, da mun xaukaka shi da su, kuma amma shi ya nemi dawwama a cikin qasa, kuma ya bi son zuciyarsa , to misalinsa kamar misalin kare ne, idan ka yi dauki a kansa ya yi lallage ko kuwa ka bar shi, ya yi lallage……”
Dan haka lallage xabi’ace ta kare
Abin tambayarmu anan shi ne: - shin kare yana yada cutuka a tsakanin al’umma?
Dangane da amsar wannan tambaya ne muka so mu kawo bayanan malamai da irin mabambanta ra’ayoyin da ke tsakaninsu.
Malam Yusuf Alh Ahmad ya yi babi guda akan wannan matsala a cikin
littafinsa mai suna:
موسوعة الاعجاز العلمي في القرءا والسنة المطهرة ص (602)
Farko ya fara kawo Hadisin Annabi [s.a.w.] wanda Imamu Muslim ya kawo daga Abuhuraira cewa:-
"وعن ابي هر يرة رضي الله عنه قال:- قال رسول الله صلي الله عليه وسلم:- "طهور اناء احدكم اذا ولغ فيه الكلب ان يغسله سبع مرات اولا هن بالتراب"
“ Manzan Allah [s.a.w] y ace: -
“Tsarkin Kwayar kowannenku idan kare ya sa baki a cikinta, shine ya wanke ta sau (7) xaya daga cikin wankin ya zama da Qasa.”
          Haka kuma a  wani Hadithi  da aka karbo daga Ibni Mugaffal, ya ce:
{Manzan Allah (S.A.W) ya ba da umarnin kashe Karnuka kuma sannan     ya ce: me ye rowanku da  Kare,
Haka kuma Annabi (s.a.w.) ya yi rangwame akan KAREN FARAUTA DA KAREN GADIN DABBOBI, sai ya ci gaba da cewa: idan kare ya sa baki a kwaryar xayanku, to ya wanke sau Bakwai xaya daga  cikin wankewar ya zamo da Qasa
Malamai sun karawa juna sani dangane da ma’anar wannan Hadithin Musmman Kalmar: - اذا ولغ الكلب                                                                                      
    Malam Ali Bassam a cikin:-
   توضيحالاحكا م شرح العمدة الاحكا م                                                                          
Yace : -
A cikin Bakin kare musamman yawunsa akawai Najasa, dan haka idan har ya sa baki a kwaryar sai an wanke sau (7) xaya da Qasa
Imamus-Shafi’I  ya ce: -
Komai na jikin kare ma Najasa ne don haka duk abin da ya shiga cikin Qwaryar daga sassan jikin kare, to sai anwanke sau (7) kamar yadda aka faxa
Amma shi Imamu Malik y ace: -
Babu wata najasa a jikin kare, ko wankewa ma da aka ce a yisau (7) to ibada ce kawai
Amma wani malami da ake kiransa Dayyyara a cikin littafinsa mai suna: -
Ya ce: -
“Binciken masna ya tabbatar da cewa shi kare yana dauke da wata guba a tare das hi y ace wasu tsutsotsi ne ke fita daga bakinsa masu cutar dad an-Adam
Amma shi mai littafin:
M. Yusuf A. Ahmad cewa ya yi: -
“Ba shakka binciken masana kimiyya ya tabbatar da cewa kare yana daga cikin Dabbobi masu yada cutuka masu hadari domin akawai wata tsutsa da take rayuwa a cikin uwar Hanjinsa, ana kiran wannan Tsutsa da (AL-MAKURAT)
Kwayoyin wannan tsutsa suna fita a cikin kashinsa, don haka idan kare ya lashi duburarsa da harshensa sai ya kwaso wannan kwayoyi zuwa kwarya ko kwanon abincin day a sansana ko kuma kwayoyin su tafi I zuwa hannun wanda duk yake muamala das hi kuma nan da nan wadannan kwayoyi cuta su kana shiga cikin uwar hanjin Dan-Adam.
Da zarar kwayoyin sun shiga uwar hanji ko hanji sa su kyankyashe sai jariran tsutsotsi su shiga ko ina a jikin Dan-Adam ta hanyar jinni musamman cikin hamtar Dan Adam
Irin wadannan tsutsotsi sukan taru guri guda a sassan jiki su samar da wata jaka matara runga tar ashen lafiya a sassan jiki ana kiran wannan jaka da: -
Haka kuma irin wanan cutar tanada hadarin gaske a jiki musamman idan cutar ta kama kwakwalwa ko sassan zuciya ko wata gaba ta jiki sau da dama idan wannan cuta ta kama jiki sai an yi tiyata.
Haka kuma matsala ta biyu ta kare da yake yadawa, ga Al-umma it ace: - a cutar kare mai haddasa zazzabi wacce yake yadawa ta hanyar yawunsa ta hanyar lasa kuma nan da nan wannan cuta ta ke haduwa a tsakanin Al-umma.
To sai dai kuma ita wannan cuta ta biyu da ake dauka daga yawun kare malamai masu bincike sun gano cewa: -
“Ba kowane kare ne yake dauke da wannan cuta ba, Karen da yake dauke da wannan cuta shi ake kira da
Ma’ana: - masifaffen kare ko kare mai yawan cin kare ko kare mai yawan kai farmaki da sauransu.
WANKE KWARYA SAU BAKWAI DAYA DAGA CIKI YA ZAMA DA KASA
Akwai maganganun malamai da dama a kan wannan mas’ala ta wanke kwaryar da kare ya sansana da ruwa da kasa.
-         Wasu suna garin yin hakan wajibine? Ko kuwa don kyautata tsaftace
-         ALI BASSAM mai y ace: -
Wasu malamai suma ganin cewa sanya kasa a cikin wanki bakwai da za’ayi wa kwaryar da kare ya sawa baki kawai ibada ce, wato bin umarnin manzon Allah ne (S.A.W)
Wannan kuma shine ra’ayin Imamu MALIK.
                                                                                                   
Amma shi malam Ahmad Mursiy Usani Jauhar a cikin littafinsa: cewa ya yi: -
Sanya kasa a cikin wanke kwarya sau Bakwai hikima ce  ta futar  da Datti, domin da can larabawa ba su da sabulu shi ya sa Annabi S.A.W ya ce: a yi amfani da kasa amma a yanzu za’a iya amfani da sabulu ko makamancinsa, kuma su tsaya a matsayin kasar da aka ambata.
Haka kuma shi Khadimussunna mai littafin cewa yayi: -
Kare ya na daga cikin Dabbobin da suke yada cuta a tsakanin al,umma kuma bincikde ya nuna cewa: akwai cutuka da ba su gaza guda (50) ba wadanda ake samunsu a jikin kare, musamman a yawunsa ko a Duburarsa, kuma wadannan cutuka babu wani sinadari da yake iya konesu da gareje inba kasa ba.
Malamin ya ci gaba da cewa: - akwai wata Jami’a ta Amerika da take a kasar Labanoon, sun gudanar da wani bincike a kan: -
Tasirin kasar makabartu, a kan gawawwakin mutane wadanda suke mutuwa a sabanin cutuka masu hadari iri daban – daban wasu kanjamau, wasu teebee, wasu tinjere da sauransu.
In banda kasa tana kone irin wadannan cutukan da ake mutu das u, to da tasirin su ya dinga cutar da Rayayyu, saboda haka, hikimar Annabi S.A.W wajen a wanke kwaryar da kare ya taba daya ya zamo da kasa, ba maganceta tsafta kawaiba domin kwayoyin cutar da ke fita daga bakin kare zuwa kwayar day a sansana, ba abin da yake iya kone su da garaje in ba kasaba.

BAMBANCIN KARE DA KYANWA A WAJEN YADA CUTA:
Bisa ga bayannan da suka gabata mun fahimci cewa, kare yana yada cutuka a tsakanin Jama’a musamman ta yawunsa da abin da ke futa daga Duburarsa.
Ita kuwa kyanwa, an tambayi Annabi (S.A.W) akanta sai y ace: -
Ma’ana:
Ita kyanwa ba najasa ba ce, kadai dai ita tana daga cikin Dabbpobi masu kaiwa da komowa a cikinku.
Kuma ya kasance yana yin al-wala da guntun rowan da tasha ta rage.
Haka kuma ita kyanwa a wuri daya ne binciken masana kimiyya ta gano cewa: - akwai wasu kwayoyin cuta da suke cikin kashinta wadanda suke shiga jikin mutum suna makantar da shi.
 Ke nan wannan Daliline yasa Allah (S.W.T) ya koyar da ita/ya shiryar da ita, idan za ta yi kashi, sai ta tona rami, in ta gama kuma ta bunne, wannan ko shakka babu hikima ce daga Allah ubangiji madaukakin sarki.
SHIN ALJANU SUNA ZAMA KARNUKA HAR SU CUTAR DA DAN-ADAM?
Tabbas dalili na shari’a sun tabbatar da cewa, akwai Aljanu masu zama karnuka, ko kuma masu Nau’I irin Nau’in karnuka.
Hadisi ya tabbat riwayar Dabrane da Hakim da Baihakiy da Samadi ingantacce, manzon Allah (S.A.W) y ace: -
Ma’ana: -
“Aljanu Nau’I uku ne: -
-         Akwai nau’in da suke da Fukafukan da suke tashi sama da su,
-         Da nau’in da suke kamar macizai da karnuka,
-         Da kuma masu zama a wani bugire sukuma ta shi su yi gaba wani lokaci.

No comments:

Post a Comment