MA'ANA: "Da yawa
daga ma'abota littafi, sun yi burin mai da ku kafirai bayan kun riga kun yi
imani, kawai don hassada da ke cikinzuciyarsu, alhali hujjoji da daliali sun
tabbata cewa Addininku shine Addinin gaskiya"[1]
Haka kuma a cikin Suratun-Nisa'i aya
ta "54" Allah yana cewa:-
MA'ANA: "Kawai dai –
Yahudu – Na yi wa Annabi (S.A.W) hassada ne saboda Annabtar da Allah ya ba shi,
suna yi wa muminai Hassada saboda tabbatuwar su akan imani, to ai mun bai wa
waxanda ke gabaninku Annabta da littafi da shugabanci mai girma". Dan me
ba su yi masu Hassada ba, sai kai suka keve da ita?"[3]
Haka nan a cikin
suratul – fatahee aya ta (15) Allah yana cewa:-
MA'ANA: "Da sannu
waxanda suka qi fita tare da Manzan Allah (S.A.W0 don yin Umra lokacin
Hudaibiyya, idan kun tafi don xibar Ganima a Haibara mu yi yaqi tare da ku,
suna son canza alqawarin Allah wanda ya yiwa ma'abota Hudaibiyya ta samun
ganima a Haibara, ku ce da su kada ku biyo mu, don haka Allah ya hukunta
tuntuni, da sannu za su ce; kawai dai Hassada kuke mana don kada mu yi tarayya da
ku, sai Allah ya ce:- Su xin sun kasance ba sa fahimtar abu irin yadda ya
kamata sai xan kaxan"[5].
Hakanan Allah
maxaukakin Sarki a cikin Suratul Falaq aya ta biyar yana cewa:-
MA'ANA: "Da
sharrin mai Hassada idan ya yi Hassada"[7].
WASU DAGA CIKIN
HADISAN ANNABI (S.A.W) WAXANDA SUKA YI MAGANA A KAN HASSADA:
Kamar yadda muka gani daga cikin wasu
ayoyin Alqur'ani suna bayani akan hassada, to haka ma idan mun koma ga Hadisan
Manzonsa Manzon Tsira Annabi Muhammadu (S.A.W) za mu ga haka:
"Kada ku yi
hassada, kada ku yi zulaqen kuxi a cikin ciniki da sunan yaudara. Kada ku yi
qiyayya, kada ku juyawa junanku baya, kada sashinku yayi ciniki akan cinikin
wani, ku kasance bayin Allah 'yan uwa"[9].
Bukhari da Muslim da Abu-Dauda da
Tirmizi da Malik a Muwaxxa duk sun rawaito Hadisin in ji Aliyyullahi ibni Aliyu
Abul Wafa[10].
Haka Al-Imamut-Tirmizi: Ya fitar da
Hadisi da sanadi mai kyau daga Zubairu Allah Ya qara yarda a gar shi ya ce:-
ABUBUWAN DA KE CIKI:
- Gabartwa
- Ma'anar Hassada.
- Ayoyin Alqur'ani akan Hassada.
- Hadisan Manzan Allah (S.A.W).
- Rabe-raben Hassada
- Kambin Ido.
- Ayoyin Alqur'ani akan Ainu (Kambin Ido).
- Dalilai daga Sunna akan (Ainu) Kambin Ido.
- Maganganun Malamai akan Kambin ido.
- Qarin ma'anar Hassada.
- Bambancin Hassada da Kambin ido.
- Cutukan da Hassada ke jawowa.
- Hanyoyin gane mai kambun ido
- Alamomin cutar kambin Ido.
- Cutar kambin ido ga qananan yara.
- Hanyoyin magance Kambin Ido da Hassada.
- Hassada ta Aljanu.
- Abubuwan da suke jawo hassada.
- Kafin abin ya faru.
- Zikirin safiya da maraice.
- Labarurrukan da suka faru.
- Qoqarin yi wa Annabi (S.A.W) Hassada/Kambin Ido
- Ya cutar da xansa da Kambin ido.
- Kammalawa.
- Manazarta.
GABATARWA
بسم الله الرحمن الرحيم
الحمد لله رب العلمين، والصلاة والسلام على أشرف المرسلين، سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وأصحابه أجمعين، ورضي الله تعالى عن السادات التابعين، والعلماء العاملين، ولأئمة الأربعة الـمجتهدين، ومقلّديهم بإحسان إلى يوم الدين. أمّا بعد:
- Shugaban wannan zama mai albarka.
- Manyan Baqi.
- Manyan mahalarta wannan Muhadara mai albarka.
- Xaliban ilimi, 'yan uwana.
- Da dukkanin wanda yake wannan waje, ko yake jin mu a daidai wannan lokaci.
Ina gabatar da gaisuwa irin ta Addinin Musulunci:-
السلام عليكم ورحـمة الله وبركاته،
Da farko ina gode wa Allah Ubangiji Maxaukakin Sarki da ya azurtamu da ganin wannan lokaci da muke ciki, kuma ina yabawa 'yan kwamitin da suke shirya wannan muhadara mai albarka, domin faxakar da al'ummar Musulmi akan abubuwan da suka shafi rayuwarsu ta Addini da Mu'amala, Allah ya saka masu da alkhairi, tare da dukkan wanda yake taimakawa ta kowace irin hanya. Allah ya saka masu da alkhairi, Amin.
Haqiqa an gabatar da ni a wannan guri, domin na yi bayani a kan:
HASSADA DA IRIN CUTUKAN DA TAKE JAWOWA A TSAKANIN AL'UMMA.
To sai dai kullum na kan yi qoqarin na tunatar da 'yan uwa, cewa: kada su yi tsammanin za su ji MUHADARA irin ta malamai, domin ni ba malami ba ne, suna na dai kamar yadda ake ji, YAKUBU MAIGIDA KACHAKO, ina tare da cibiyar binciken Magungunan Musulunci da faxakarwa ta garin Kachako, wace ke da ofishi a Hotoro ramin kwalabe cikin Birnin Kano. da kuma nan garin misau unguwar alumri, Mai yiwuwa wannan shi ne dalilin da ya sa aka ba ni wannan maudu'i domin na gabatar da shi, ina roqon Allah ya taimake ni, ya kuma azurta ni da faxar abin da masu sauraron wannan Muhadara za su amfana. Amin.
MA'ANAR HASSADA:-
(a) A Harshen Larabci:
Zainuddini Arraziy, a cikin littafinsa Mukhtaris-Sihahi, cewa ya yi:z
اَلْـحَسَدُ: أَنْ تَتَمَنَّى زَوَالَ نِعْمَةِ الْمَحْسُودِ إِلَيْكَ...
HASSADA: Ita ce burin gushewar wata ni'ima daga mai ita zuwa ga mai yin Hassada.
(b) Dr. Ahmad Mustapha Mutawalla, a cikin littafinsa mai suna:
اَلْمَوْسُوعَةُ الشَّامِلَةُ فِي الطُّبِّ الْبَدِيلِ.
Ya kawo fassarar Kalmar Hassada ne kamar yadda Alhafiz ibn Hajar Al-Asqalaniy ya kawo ta a cikin littafinsa mai suna:
"فَتْحُ الْبَارِي – شَرْحُ الْبُخَارِي" cewa:
اَلْـحَسَدُ: تَـمَنَّـى زَوَالِ النِّعْمَةِ مِنَ الْمُنْعَمِ عَلَيْهِ .
HASSADA: Shi ne kwaxayin rushewar wata ni'ima daga wanda aka yi wa wata ni'ima. Ko kuma kwaxayin dawowar ni'imar wanda aka yiwa ni'ima zuwa gare shi.
(c) Shi kuwa Assheak Mohammad bin Saleh Al-Usaimeen, xaya daga cikin limaman Sa'udiyya, a cikin Sharhin da ya yi wa littafin "AL-ARABA'INAN NAWAWIYYA", cewa ya yi:-
Hassada, shi ne kwaxayin gushewar wata ni'ima da Allah ya yiwa wani, wannan ni'ima ko dai ta kasance ta kuxi ko matsayi, ko ilimi, ko wani abin daban .
Shi kuwa Malam Aliyullahil bini Aliyyul-Wafa a cikin littafinsa mai suna: "اَلدَّوَاءُ الْقُرْآنِي لِلْجِنِّ وَالْمَسِّ الشَّيْطَانِي" cewa ya yi:-
اَلْـحَسَدُ: هُوَ كَرَاهَةُ النِّعْمَةِ وَحُبُّ زَوَالِـهَا عَنِ الْمُنْعَمِ عَلَيْهِ.
HASSADA: Shi ne qin wata ni'ima, da kuma son gushewar ta daga wanda aka yi wa ni'imar".
A ta qaice dai, duk lokacin da mutum ya ji a ransa cewa: ba ya son ya ga waninsa ya mallaki wani abu na rayuwa, kamar dukiya, ko ilimi, ko dai wani abu na jin daxi, to wannan mutum sunansa mai hassada.