Sunday, 24 March 2013

TARBIYYA


TARBIYA TA MUAMALA
MUHIMMAN MUSALAI NA KYAKYAWAR MU’AMALA  SUNE:
ü Cika al’kawari.
ü Kamewa.
üGaskiya
üAmana 
MUSALAI NA MUNANAN MU’AMALA
 
* Rashin Gaskiya
*
* Rashin   Amana

TARBIYYA


TARBIYA TA DABIA
Musalai na  Kyawawar Dabia
Girmama na Gaba
Hakuri
Tausayi
Juriya
Musalai na Munanan Dabi’u
ØRaina na Gaba
ØRashin Hakuri
ØRashin Kunya
ØRashin Tausayi
ØRashin  kwazo

Wednesday, 20 March 2013

TARBIYYA

GABATAR DA BAYANI    AKAN
TARBIYYA
AYAU ZAMU TATTAUNA  KAN RAYUWAR YARA A DUNIYAR MU AYAU
A FAGGEN TARBI
RABE-RABEN TARBIYA:
Tarbiya ta kasu kashi tara (9):-
1.Tarbiya ta Ruhi
2.Tarbiya ta Jiki
3.Tarbiya ta Dabi’a
4.Tarbiyar  Gado
5.Tarbiyar  Mu’amala
6.Tarbiyar Gurin Zama
7.Tarbiya ta Addini
8.Tarbiyar Kame kai
9.Tarbiyar Tunani


 



Saturday, 9 March 2013

HASSADA 2.


KAXAN DAGA AYOYIN ALQUR'ANI WAXANDA ALLAH YA AMBACI HASSADA A CIKINSU:
Allah ya ambaci Kalmar Hassada a gurare da dama:-
SURAH:             AYA:
-         Albaqara              109
-         Annisa'i               54
-         Alfathi                 15
-         Alfalaq                5
A cikin suratul – Baqara, aya ta (190) Allah yana cewa:        
                                                                          البقرة: ١ - ١٠٩
MA'ANA: "Da yawa daga ma'abota littafi, sun yi burin mai da ku kafirai bayan kun riga kun yi imani, kawai don hassada da ke cikinzuciyarsu, alhali hujjoji da daliali sun tabbata cewa Addininku shine Addinin gaskiya"[1]
          Haka kuma a cikin Suratun-Nisa'i aya ta "54" Allah yana cewa:-
                  ﭱﭲ                           [2]
MA'ANA: "Kawai dai – Yahudu – Na yi wa Annabi (S.A.W) hassada ne saboda Annabtar da Allah ya ba shi, suna yi wa muminai Hassada saboda tabbatuwar su akan imani, to ai mun bai wa waxanda ke gabaninku Annabta da littafi da shugabanci mai girma". Dan me ba su yi masu Hassada ba, sai kai suka keve da ita?"[3]
Haka nan a cikin suratul – fatahee aya ta (15) Allah yana cewa:-
                 ﯯﯰ           ﯵﯶ                ﯾﯿ       ﰂﰃ                          [4]
MA'ANA: "Da sannu waxanda suka qi fita tare da Manzan Allah (S.A.W0 don yin Umra lokacin Hudaibiyya, idan kun tafi don xibar Ganima a Haibara mu yi yaqi tare da ku, suna son canza alqawarin Allah wanda ya yiwa ma'abota Hudaibiyya ta samun ganima a Haibara, ku ce da su kada ku biyo mu, don haka Allah ya hukunta tuntuni, da sannu za su ce; kawai dai Hassada kuke mana don kada mu yi tarayya da ku, sai Allah ya ce:- Su xin sun kasance ba sa fahimtar abu irin yadda ya kamata sai xan kaxan"[5].
Hakanan Allah maxaukakin Sarki a cikin Suratul Falaq aya ta biyar yana cewa:-
             [6]
MA'ANA: "Da sharrin mai Hassada idan ya yi Hassada"[7].
WASU DAGA CIKIN HADISAN ANNABI (S.A.W) WAXANDA SUKA YI MAGANA A KAN HASSADA:
          Kamar yadda muka gani daga cikin wasu ayoyin Alqur'ani suna bayani akan hassada, to haka ma idan mun koma ga Hadisan Manzonsa Manzon Tsira Annabi Muhammadu (S.A.W) za mu ga haka:
          Ga kaxan daga cikinsu kamar haka:-
1)Manzon Allah (S.A.W) ya ce:-
"لاَ تَحَاسَدُواْ وَلاَ تَنَاجَشُواْ، وَلاَ تَبَاغَضُواْ، وَلاَ تَدَابَرُواْ، وَلاَ يَبِعْ بَعْضُكُمْ عَلَى بَيْعِ بَعْضٍ، وَكُونُواْ عِبَادَ اللهِ إِخْوَانًا"[8]. رواه البخاري ومسلم وأبو داود والترمذي.
Ma'anar Hadisin:
"Kada ku yi hassada, kada ku yi zulaqen kuxi a cikin ciniki da sunan yaudara. Kada ku yi qiyayya, kada ku juyawa junanku baya, kada sashinku yayi ciniki akan cinikin wani, ku kasance bayin Allah 'yan uwa"[9].
          Bukhari da Muslim da Abu-Dauda da Tirmizi da Malik a Muwaxxa duk sun rawaito Hadisin in ji Aliyyullahi ibni Aliyu Abul Wafa[10].
          Haka Al-Imamut-Tirmizi: Ya fitar da Hadisi da sanadi mai kyau daga Zubairu Allah Ya qara yarda a gar shi ya ce:-
قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "دَبَّ إِلَيْكُمْ دَاءُ اْلأُمَمِ قَبْلِكُمْ اَلْـحَسَدُ وَالْبَغْضَاءُ".
 Ma'ana: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Cutar al'umman da suka gabace ku ta shigo cikinku, Hassada da qiyayya".


[1] -   الصابوني، صفوة التفاسير، تفسير سورة البقرة، (159) المجلّد الأول، ص:
[2] - النساء: ٥٤
[3] -  الصابوني، صفوة التفاسير، التفاسير، تفسير سورة البقرة، (159) الـمجلد الأول، ص:
[4] - الفتح: ١٥
[5] -  الصابوني، صفوة التفاسير، تفسير سورة الفتح.
[6] - الفلق: ٣
[7] - الصابوني، صفوة التفاسير، تفسير سورة الفلق، الـمجلد الثالث، ص
[8] -
[9] -
[10] -

Friday, 8 March 2013

"HASSADA DA CUTUKAN DA TAKE JAWOWA GA AL'UMMA

ABUBUWAN DA KE CIKI: - Gabartwa - Ma'anar Hassada. - Ayoyin Alqur'ani akan Hassada. - Hadisan Manzan Allah (S.A.W). - Rabe-raben Hassada - Kambin Ido. - Ayoyin Alqur'ani akan Ainu (Kambin Ido). - Dalilai daga Sunna akan (Ainu) Kambin Ido. - Maganganun Malamai akan Kambin ido. - Qarin ma'anar Hassada. - Bambancin Hassada da Kambin ido. - Cutukan da Hassada ke jawowa. - Hanyoyin gane mai kambun ido - Alamomin cutar kambin Ido. - Cutar kambin ido ga qananan yara. - Hanyoyin magance Kambin Ido da Hassada. - Hassada ta Aljanu. - Abubuwan da suke jawo hassada. - Kafin abin ya faru. - Zikirin safiya da maraice. - Labarurrukan da suka faru. - Qoqarin yi wa Annabi (S.A.W) Hassada/Kambin Ido - Ya cutar da xansa da Kambin ido. - Kammalawa. - Manazarta. GABATARWA بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العلمين، والصلاة والسلام على أشرف المرسلين، سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وأصحابه أجمعين، ورضي الله تعالى عن السادات التابعين، والعلماء العاملين، ولأئمة الأربعة الـمجتهدين، ومقلّديهم بإحسان إلى يوم الدين. أمّا بعد: - Shugaban wannan zama mai albarka. - Manyan Baqi. - Manyan mahalarta wannan Muhadara mai albarka. - Xaliban ilimi, 'yan uwana. - Da dukkanin wanda yake wannan waje, ko yake jin mu a daidai wannan lokaci. Ina gabatar da gaisuwa irin ta Addinin Musulunci:- السلام عليكم ورحـمة الله وبركاته، Da farko ina gode wa Allah Ubangiji Maxaukakin Sarki da ya azurtamu da ganin wannan lokaci da muke ciki, kuma ina yabawa 'yan kwamitin da suke shirya wannan muhadara mai albarka, domin faxakar da al'ummar Musulmi akan abubuwan da suka shafi rayuwarsu ta Addini da Mu'amala, Allah ya saka masu da alkhairi, tare da dukkan wanda yake taimakawa ta kowace irin hanya. Allah ya saka masu da alkhairi, Amin. Haqiqa an gabatar da ni a wannan guri, domin na yi bayani a kan: HASSADA DA IRIN CUTUKAN DA TAKE JAWOWA A TSAKANIN AL'UMMA. To sai dai kullum na kan yi qoqarin na tunatar da 'yan uwa, cewa: kada su yi tsammanin za su ji MUHADARA irin ta malamai, domin ni ba malami ba ne, suna na dai kamar yadda ake ji, YAKUBU MAIGIDA KACHAKO, ina tare da cibiyar binciken Magungunan Musulunci da faxakarwa ta garin Kachako, wace ke da ofishi a Hotoro ramin kwalabe cikin Birnin Kano. da kuma nan garin misau unguwar alumri, Mai yiwuwa wannan shi ne dalilin da ya sa aka ba ni wannan maudu'i domin na gabatar da shi, ina roqon Allah ya taimake ni, ya kuma azurta ni da faxar abin da masu sauraron wannan Muhadara za su amfana. Amin. MA'ANAR HASSADA:- (a) A Harshen Larabci: Zainuddini Arraziy, a cikin littafinsa Mukhtaris-Sihahi, cewa ya yi:z اَلْـحَسَدُ: أَنْ تَتَمَنَّى زَوَالَ نِعْمَةِ الْمَحْسُودِ إِلَيْكَ... HASSADA: Ita ce burin gushewar wata ni'ima daga mai ita zuwa ga mai yin Hassada. (b) Dr. Ahmad Mustapha Mutawalla, a cikin littafinsa mai suna: اَلْمَوْسُوعَةُ الشَّامِلَةُ فِي الطُّبِّ الْبَدِيلِ. Ya kawo fassarar Kalmar Hassada ne kamar yadda Alhafiz ibn Hajar Al-Asqalaniy ya kawo ta a cikin littafinsa mai suna: "فَتْحُ الْبَارِي – شَرْحُ الْبُخَارِي" cewa: اَلْـحَسَدُ: تَـمَنَّـى زَوَالِ النِّعْمَةِ مِنَ الْمُنْعَمِ عَلَيْهِ . HASSADA: Shi ne kwaxayin rushewar wata ni'ima daga wanda aka yi wa wata ni'ima. Ko kuma kwaxayin dawowar ni'imar wanda aka yiwa ni'ima zuwa gare shi. (c) Shi kuwa Assheak Mohammad bin Saleh Al-Usaimeen, xaya daga cikin limaman Sa'udiyya, a cikin Sharhin da ya yi wa littafin "AL-ARABA'INAN NAWAWIYYA", cewa ya yi:- Hassada, shi ne kwaxayin gushewar wata ni'ima da Allah ya yiwa wani, wannan ni'ima ko dai ta kasance ta kuxi ko matsayi, ko ilimi, ko wani abin daban . Shi kuwa Malam Aliyullahil bini Aliyyul-Wafa a cikin littafinsa mai suna: "اَلدَّوَاءُ الْقُرْآنِي لِلْجِنِّ وَالْمَسِّ الشَّيْطَانِي" cewa ya yi:- اَلْـحَسَدُ: هُوَ كَرَاهَةُ النِّعْمَةِ وَحُبُّ زَوَالِـهَا عَنِ الْمُنْعَمِ عَلَيْهِ. HASSADA: Shi ne qin wata ni'ima, da kuma son gushewar ta daga wanda aka yi wa ni'imar". A ta qaice dai, duk lokacin da mutum ya ji a ransa cewa: ba ya son ya ga waninsa ya mallaki wani abu na rayuwa, kamar dukiya, ko ilimi, ko dai wani abu na jin daxi, to wannan mutum sunansa mai hassada.