Saturday, 20 April 2013

MATSALOLIN MA'AURATA NA MUSAMMAN

GABATAR DA TAKARDA
DAGA
{DR.} YAKUBU MAIGIDA KACHAKO
MUKADDASHIN BABBAN KWAMANDAN HISBAH NA JIHAR KANO MAI KULA DA AIYYUKAN YAU DA KULLUM

MAI TAKEN
 مشاكل الزوجين الخاصة

MATSALOLIN MA’AURATA NA MUSAMMAN.

[SPECIAL PROBLEMS OF
COUPLES]


SHIMFIXA
MATSAYIN RASHIN LAFIYA GA XAN ADAM
Ita rashin lafiya Allah na sanyata a jikin xan-adam ne saboda abubuwa kamar haka:
1.     Qankarar Zunubai
Kamar yadda Allah ta’ala yake cewa:

((ما أصابكم من مصيبة فبما كسبت أيديكم ويعفو عن كثير)) [سورة الشورى: 30].
Ma’ana:
“Duk abin da ya sameku dangane da cutuka da masifu, na daga abin da kuka aiwatar da hannayenku, Ubangiji na yi muku rangwame akan abubwa masu yawa…”
"وما صييب المسلم من نصب ولا وصب ولا هم ولا أذى ولا غم حتى الشوكة يشاكها، إلا كفر الله من خطاياه". رواه البخاري.
Ma’ana:
Babu wani abu da zai sami muslumi na gajiya ko rashin lafiya ko damuwa ko wata cuta ko damuwa, ko da qayar da zai taka, face sai Allah ya kankare wani vangare na kura-kuransa (zunubai).
Don haka duk wanda Allah ya jarraba da wata cuta ko rashin lafiya, ana sa ran zunubansa ake kankare masa da ita.
2.     Xaukaka darajar mara lafiya da qara yawan ladansa.
Domin ya tabbata Manzon Alalh (S.A.W) ya ce:
"ما من مؤمن يشاك شوكة فما فوقها إلا كتبت له بها درجة ومحيت عنه بها خطيئة". رواه مسلم.
Ma’ana:
Babu wani mumini da zai taka qaya ko wani abin da ya darammata face sai an rubuta masa lada akan hakan, a kuma goge masa kurakurai.
3.     Tana zama sababin shigarsa aljanna.
"خفت الجنة بالمكاره وحفت النار بالشهوات". رواه البخاري ومسلم.
Ma’ana:
Aljanna an kewayeta da ababan qi, wuta kuma an kewayeta da ababan sha’awa.
Abinda ake nufi da (المكار) shi ne dukkan abinda rai baya so.
4.     Kuvuta ga barin shiga wuta:
Hadisi ya tabbata daga Abi Huraira (R.A) Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه عاد مريضا من وعك كان به فقال له: أبشر فإن الله عز وجل يقول: (هي ناري أسلطها على عبدي المؤمن في الدنيا، لتكون حظه من النار في الآخرة). أخرجه أحمد وغيره.
Ma’ana:
Manzon Allah (S.A.W) ya gaishe da wani marar lafiya wanda ke cikin zafin zazzavi sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi: (Ka yi farin ciki, domin Allah maxaukakni sari yana cewa; (Wuta tace da nake sanyata ga bawana mumini a rayuwarshi ta duniya, don ta kasance kasonsa na wutar lahira).
5.     Tunatar da bawa irin ni’imomin Ubangiji na baya da waxanda ake ciki.
6.     Tunatar da bawa iri halin da ‘yan uwansa marasa lafiya suke ciki.
7.     Tsarkake zuciya daga bari girman kai da jiji da kai.

KAYAN SA MAYE NA GARGAJIYA


GABATAR DA TAKARDA MAI TAKEN

                               KAYAN SA MAYE NA GARGAJIYA,
DA ILLOLIN
RANA:-        13/4/2013
GURI:-          AFIRKA HOUSE        
LOKACI:-    10:OOAM

SHIRYAWA DA XAUKAR NAUYI:-        
                                                          {CWYI} CARE WOMEN AND YOUTH     INITIATIVE



MAI GABATARWA:-                       {DR.} YAKUBU MAIGIDA KACHAKO
                                                                 DCG/OPS HISBAH KAN
1434AH=201




GABATARWA
Ba shakka al’amarin amfani da kayan sa maye ya zama rowan dare gama duniya, domin babu wata Nahiya da ba a shaye-shaye, sai de a sami bambance-bambance saboda yanayin wayewa, ko tattalin arzuqi, ko kuma kokarin shugabannin wannan Nahiya wajen daqile harkar shaye-shaye.
Wannan gangami da wannan qungiya take shiryawa a qarqashin jagorancin Maigirma Matar Mai girma Mataimakin Shugaban Qasa, ya zo dai-dai da lokacin Al’ummar Nageriya ke buqatarsa. Sanna yayi dai-dai da yunqurin gwamnatin jahar kano na yaqi da kaya sa Maye, a aikace.
Abubuwa uku ake gudu game da Illar shaye-shaye, su ne:-
1.     Shigar Mata harkar shaye-shaye,
2.     Shigar qananan Yara. Da
3.     Shigar Matasa harkar shaye-shaye.

Ø Illar shaye-shaye a gurin Mata ita ce:- “Rushewar Tarbiyya”  saboda su ke xaukar ciki, shayarwa, reno da Tarbiyya in suka zama ‘yammaye akwi Matsa….
Ø Yara daga primary, zuwa  Sakandare, idan suna shaye-shaye, da wuya suke  iya dainawa, ko da sun tafi Jami’o’i, kuma su a ke sa ran su zama shugabanni nan gaba, ko kuma su zama Jami’an tsaro, to, kuwa  idan ya zama tsaron lafiya da dukiyar masu hankali, ya koma hannun Yara ko Matasan da ke shaye-shaye, masu rushasshen hankali, to, ba shakka a kwai tashin hankali, Allah ya kiyaye amen.
Danhak mu muna goyon bayan irin wannan yunquri a matakai da ban da ban,kuma matakan da gwamnatin jahar kano take xauka na sama wa Matasa aiyyukan yi, ko shakka babu, zai magance shaye-shaye.
Sai de kawai a ci gaba da jajircewa domin yaqi da kayan sa maye, a gurin masu sha da sayarwa, kamar masu wankin gyanbo ne da mai gyanbo, kullum mai gyanbo bay a gane sonsa a ke sai bayan ya warke, haka mai shan kayan maye da mai sayarwa suke.
  
  TARIHIN KAYAN SA MAYE A DUNIYA:
        Ba a samu wani takamaiman gamsasasshen bayani ba, da yake nuna asalin faruwar xabi'ar shaye-shayen miyagun qwayoyi ko amfni da kayan sa maye ba.
        Qoqarin neman magani da jarrabawa, ya fara ne tun lokacin da xan Adam ya fara rayuwa, rayuwar xan Adam ita ce faruwar amfani da magani, domin tun zamani mai tsawo lokacin da xan Adam ya fara rayuwa, an samu yana sarrafa itatuwa da tsirrai domin magance cutukan da suka dame shi, daga cikin itatuwan da yake sarrafawa, har ya samo waxanda za su gusar da hankalinsa, ko su sa shi farin ciki, ko su qara masa qarfin jiki, ko kuma ya yi amfani da su, domin abin da ya shafi sihiri.
        Ana cikin wannan rayuwa ne, malamai suka ci gaba da bincike domin tantance irin waxancan itatuwa da tsirrai, har suka kai ga ware masu sa maye da masu kashe zafin ciwo da raxaxi, da masu sa barci, da waxanda ke rage zafin damuwa da xan Adam ke samun kansa a ciki. Wannan ne ya jawo aka dinga shuka irin waxannan tsirrai, da kuma samar da cibiyoyin sarrafa su, aka dinga daidaita wasu masu tsanani daga cikinsu domin su dace da jikin xan Adam, to, waxannan su ake kira kayan sa maye, waxanda aka samo asalinsu daga tsirrai, da maganin gargajiya, kamar:-
WIWI(GANYE), OPIYON, KOKEN, da sauransu.
Daga waxancan sarrafe-sarrafe ne duniyar kimiyya ta samar da sababbin kayan sa maye, ta hanyar: QWAYOYI, "KAFSO, WAXANDA AKE SHAKAWA TA HANCI, KO KUMA SHA TA BAKI" kuma dukkansu suna da illoli iri xaya da wanda waxancan na tsirran ke da su.
        Akwai savanin malamai dangane da iyakance tarihin kayan maye a Duniya, yaushe ne a ka san su? Yaushe aka fara amfani da su? Ta yaya suka yaxu a Duniya? Sannan abin da ya fi bayyana ita ce tabar wiwi, domin ita ce kan gaba da xan Adam ya fara sani kafin ya san sauran kayan maye.
  Break A'idul Karni a cikin littafinsa المخدرات الخطر الإجتماعي الداهم""
ya ce:
        "Ana qaddara asalin samuwar kayan sa maye, tun shekaru (5,000) kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) kuma an fara samun sa ne a vangaren Asiya ta kudu da gabacin kogin (البحر الأبيض المتوسط) wato "White Middle Sea".

"Mutane, ba su fahimci (KOKEN DA OPIYON" waxanda ake samunsu daga tsirrai da itatuwan gargajiya ba, sai a farko-farkon qarni na (20). Lokacin da wani mutumin qasar "GERMANY" da wasu mutane biyu na qasar "FARANSA" suka qirqiro wani magani mai sa nishaxi daga (OPIYON) kuma shi mutumin (JAMUS) xin shi ya sa masa suna (SIRATORINO) daga sunan marofin, mai dangantaka da marofis, a yaren (GIRKAWA) kuwa: Kalmar tana nufin (NA'URAR TUNANI). An ci gaba da amfani da marofin a matsayin magani mai sanya nishaxi ga jiki, har zuwa shekarar (1861-1875) lokacin da aka yi yaqin cikin gida na Amirka, (American Civil War) aka gabatar da marofin ga sojojin Amerika domin ya sauqaqa masu zafin raunin da suka samu a wannan yaqin, daga nan su kuma sai suka yawaita amfani da shi, har ya zama kayan sa maye a gare su.
        Haka kuma sojojin Rasha da suka yaqi Faransa a shekara ta (1870) da kuma sojojin da suka yi yaqin Duniya na farko (1912-1918) a cikinsu an sami adadi mai yawa na mashaya marofin a qasashen America da Turai(1).
        Haka kuma a shekara ta (1889) wasu malamai na qasar (INGILA) suka samar da sabon bincike a kan wancan magani na (MAROFIN) wanda ya samar da adadi mai yawa na masu maye daga sojojin Amirika da Turai, suka kira sunan binciken nasu da (DAY-ISTIL-MOROFIN) aikinsa yi wa masu shan (OPIYON DA MOROFIN) magani, a wajen sayarwa sai ake kiran sa da (HIROYIN) a inda aka dinga fitar da shi a matsayin magani, har zuwa shekara ta (1898) a inda aka kafa Kamfani na musamman mai suna (BAYAR ALMANIYA).
        A farkon fitowarsa ana amfani da shi ne, don warware matsalar mashaya (Morfin da Opiyon) kamar yadda aka faxa a baya, har malaman qasarsu suke ganin kamar maganin ba shi da wata illa, amma daga baya sai 'yan fashi da waxansunsu, suka gano ya fi kowanne kayan sa maye amfani a gunsu.
        Yaxuwar Hiroyin "HEROIN" a duniya ya samo asali ne daga sojojin (INGILA) da (JAPAN) kuma su ke qarfafa guiwa wajen sayar da ita da kuma fataucinta, har zuwa lokacin da aka yi yaqin Duniya na biyu.
        Haka kuma, qasashen AMERICA da MISRA, da CHINA, sun taimakawa wajen sayar da (HIROYIN) a inda China ta zama wata cibiya wajen samar da ita.
        Amma dangane da Hodar Iblis (Koken) Duniya ta gano tasirinta wajan sa maye ne a shekara ta (1876) sai dai ita ma a farkon samar da ita, an yi ta ne domin magance rauni. Ba'a gurvata hanyar amfani da (Koken) ba sai a shekara ta (1890) lokacin da (PERU) suka kafa kamfanin samar da ita, da fitar da ita zuwa qasashen waje, Hakan ta faru ne a tsakanin baqaqen fata mazauna qasar (Amirika). Daga nan sai mawaqa da masu harkar funa-funai, suka xauki Hodar iblis/Koken a matsayin kayan sa maye.


Amma dangane da (GANYE) kuwa wato (TABAR WIWI) wadda a yanzu 'yan zamani musamman matasa, suke yawan amfani da ita, kuma suke ba ta sunaye iri-iri kamar:-
-         Karas.
-         Marijuwana.
-         Bahanij.
-         Kaifu,
-         Daja.
-         'Yarmo.
-         Indian – hemp
-         Ganye.
-         Kaya.
-         Igbo
-         Stone
-         Hashis
-         Ganja
-         Grass     d.s.
Kusan kowa ya amince da cewa, ita ta fi kowane kayan maye daxewa a Duniya. Kuma ita ce aka fi amfani da ita ko'ina cikin duniya.
        Ana samun tabar Wiwi ne daga itacen (القنب والتفرز) (Canabis Sativa) a jikin itaciyar taba wiwi, akwai huda da ganye, kuma da wannan ganyen ne ake yin taba wiwi, a can baya zamanin magabata, an fi shuka ta a qasar indiya, da manyan qasashen Asiya da Afrika da kuma America(1).
        M. Mustapha Abbasiy a cikin littafinsa mai suna
 (أسرار المخاطرة التي تنتج عن تدخين السجائر والحشيشه...)
Ya ce:- "Binciken masana na Duniya ya tabbatar da cewa: "A duk cikin mutum bakwai na Duniya, za a sami guda mai shan tabar wiwi, ko kuma wanda ya tava sha"(2).
        Tun shekaru (2733) kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) qasar China suka fara bincike a kan taba wiwi, ta hanyar (Akarabazin) kuma suke amfani da ita, har abin ya watsu izuwa qasashen Misra, da Indiya, da Greak, da Afrika, da kuma yankin Larabawa.
        A qasashen Turai kuwa Faransa ce ta rungumi xabi'ar amfani da tabar wiwi, saboda sojojin da suka dawo daga yaqin Barnabat a Misra, su suka zo masu da ita.
        An gano tabar wiwi a matsayin xaya daga cikin kayan sa maye ce tun a qarni na (10) kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) haka abin ya ci gaba da yaxuwa ta matakai daban-daban a qasashen Duniya.
        Amma Girkawa su ne farkon waxanda suka siffanta tabar wiwi ta hanyar zane, an kira wannan aiki nasu da suna: (DIYOSOKORIDIS) daga hannunsu ne likitocin larabawa da na Farisa, suka Siffanta wannan tsiro (Tabar wiwi) har su mutanen Farisa suka yi bincike, suka gano irin yanayin mayen da tabar wiwi take haddasawa.




KAYAN SA MAYE NA GARGAJIYA
Su kayan sa maye, sun kasu kashi-kashi, gwargwadon yadda yanayin jama'a yake da yanayin mazauni, da ilimi, da tarbiyya, da yanayin tattalin arziqin yankin yake. Amma masana wannan fannin sun raba kayan sa maye zuwa rukuni-rukuni, kuma daga cikinsu akwai masu sa mayen kai tsaye, akwai waxanda sai an yi amfani da su fiye da kima, sannan za su sa mayen, a kwai kuma waxanda xaukar lokaci wajen amfani da su ke sa su dinga sanya maye.
 Haka kuma akwai kayan mayen da ke iya dakatar da harkar jiki, ko ya motsar da ita, akwai kuma masu tasiri ga hankali da jiki, kamar:-
-         Sanya Buguwa.
-         Sanya ruxewa.
-         Shiga halin matsanancin maye.
-         Sanya matsanancin Barci. Ko sanya rashin barci.

1.   Rukunin kwayoyi ko magunguna (ILLICET DRUGS).

2.   Rukunin masu tiriri da bin iska (VOLATILE SUBSTANCES/VOLATAYAL SABTANCES)
-         Rukunin kway Petrolium – (Fetur).
-         Glue – (Gulu)
-         Rubber solution – (Sholisho).
-         Ingine Oil – (injin oyil)
-         Crosene – (Kalanzir)
-         Liquid Paraffin (Lukuy Farafin)
-         Correction Flued – (Korrektin flu)
-         Sucudine –

3.   Rukunin sinadarai (CHEMICAL)
-          Dyes.
-         Fartelizer.
-         Mahabbalan.
-         Gishirin lalle.
-         Cocaine – (Hodar Iblis)
-         Canabies/India-hemp/Marijuwana/wiwi/karas/bahanij/Daja/ Kaif/'Yarmo/Ganye    d.s.

4.   Rukunin wasu nau'o'i na daban (MISLENIOUS/MISLINIYOS).

           - wannan vangare shi ne vangaren d azan yi jawabi na a kansa,  kuma ya shafi kayan sa maye na daban, waxanda ba su shiga cikin waxancan rukunin ba kamar:-
ABUBUWAN GARGAJIYA MASU SANYA MAYE:
Kamar yadda muka faxa a can baya cewa:-
Kowacce nahiya ta jama'a tana da hanyoyin da take qiriqrar abubuwan da suke iya jawo maye, ga jama'arta, ko dai don wayewar da suka samu, ko kuma tsadar rayuwa, ko kuma nisan da suka yi ga kayan sa maye na zamani, haka su ma al'ummar Hausawa ko kuma al'ummar da ke zaune a qasar Hausa, suna da dabarun qirqirar kayan mayen da ba za ka sami irinsa a wata nahiyar ba.
Mashayan qasar Hausa sukan yi amfani da wasu abubuwa da a zahirinsu ko asalinsu ba kayan sa maye ba ne, amma an canza su an mai da su kayan sa maye.
Haka kuma kamar yadda larabawan jahiliyya suke yin amfani da dabino da inibi don yin giya, to haka su ma maguzawan da ke zaune a wasu vangarori na qasar Hausa suke yin amfani da Dawa da wasu nau'o'i na hatsi domin yin giya, kuma da irin wannan hatsi ne suke sarrafa nau'o'in giya iri daban-daban kamar:-
-         Burkutu (Hatsi).
-         Bammi (Ruwan kwakwa)
    -   Tsama-tsama (Hatsi) d.s.
 GA IRE-IREN ABUBUWAN DA AKE AMFANI DA SU A MATSAYIN KAYAN SA MAYE A QASAR HAUSA:
1.   Kashin qadangare (farin)
2.   'Ya'yan Darbejiya.
3.   Zaqami/Babba juji
4.   Zurman.
5.   Bi-ni-da zugu.
6.   Bula.
7.   Lalle (saiwarsa).
8.   Hankufa (Tana sa tsaurin rai da kuma son yin faxa ita suke bai wa tsuntsu kanari domin ya yi ta kuka ba tare da gajiya ba).
9.   Ruwan kwata.
10.Icen Kukkuki.
11.Gunar shanu (tana da xaci kuma tana sa gudawa)
12.Xan-kamaru (maganin barci)
13.Mur (Yana da xaci zai iya lalata hanta).
14.Takardar Jarida.
15.Kyankyaso (kafata).
16.Turirin Masai.
17.Gadagi.
18.Tushiyar dawa
19.Qwaxo (Ruwan bayansa guba ne wanda maciji ke sha domin samun dafi).
20.Igiyar-kaba.
21.Maganin sauro na (Hayaqi)
22.Cefane(Haxa rukunin magunguna).
23.Tsumi (haxa rukunin kayan maye).
24.Omo.
25.Fiya-fiya.
26.Kananzir.
27.Hoda gas.
28.Tokar Taba.
29.Kan ashana
30.Kashin Jaki.
31.Kashin vera.
32.Sholusho (Ya fi komai haxari domin kala shida (6) ne, guda biyu (2) ne kawai ake yin faci da su, amma sauran duk shan su ake, kuma  ya fi sauqin samu(1).
Haka kuma shi babba juji wato zaqami, an daxe ana amfani da shi a matsayin abu mai sa maye musamman ma a wuraren bukukuwan Hausawa, har ma sakkwatawa sukan yi masa waqa yayin da ake biki, misali:-
33."NI BA NI SHAN BABBA JUJI,
34.SAI RANDA 'YATA TAH HAIFE,
35.KO RANDA 'YA TA TAH HAIFE,
36.SAI NAI HURA IN AZA NONO,
37.IN XAUKI XAN XA IN GORE,
38.IN HAUKACE IM BI DAJI".
39.                       Waxannan su ne kaxan daga cikin abubuwan da ake amfani da su a wani vangare na qasar Hausa a matsayin kayan sa maye.

HANYOYIN MAGANCE SHAYE-SHAYE GA MATASA
        Babban burin kowacce qasa ko jiha shi ne so take ta ga 'yan –qasarta sun zauna lafiya, tare da cikakken hankali da bin doka, wannan shi zai sa a sami zaman lafiya da ayyukan cigaba a kowacce nahiya.
        Haka kuma matasa su ne qashin bayan cigaban kowacce al'umma idan har sun gyaru, amma idan suka lalace, sun zama haxarin rayuwar kowacce nahiya, kuma babbar hanyar lalacewar matasa ita ce:-
        (Shaye-shaye), idan har matasan gari, suna shaye-shaye to za a iya samun kowanne irin nau'i na matsala a wannan gari, kamar:-
-         Rashin bin doka.
-         Aikata miyagun laifuka.
-         Kawo cikas ga ayyukan raya qasa.
-         Rashin Tarbiyya, da kuma
-         Lalacewar Nasaba, ta fuskar haihuwar 'ya'ya marasa cikakkun iyaye.

Ko shakka babu ya zama wajibi kowacce qasa ko jiha, ko gari, qauye ne ko birni, ya tashi tsaye domin nemo hanyoyin magance matsalar shaye-shaye ko amfani da kayan sa maye, wannan ita ce maslaha, da kuma zaman lafiya. A qarqashin wannan bincike na yi nazarin wasu hanyoyi da nake ganin idan an bi su, za a magance wannan mummunar xabi'a, da ta addabi duniyar matasan wannan zamani da muke ciki.
        Hanyoyin ga su kamar haka:-
1-WA'AZI DAGA MALAMAI:-
        Wa'azin malamai wata babbar hanya ce da za ta taimaka wajen magance matsalar shaye-shayen ga matasa.
2-BAIYANAWA DA YAYATA HUKUCIN KAYAN SA MAYE A MUSLUNCI.
3-GUDUNMAWAR IYAYE DA 'YAN UWA:
        Iyaye su kula da tarbiyyar 'ya'yansu tun daga neman Aure, da goyon ciki, da reno, da lura da abokansu idan sun fara tasowa
4-GUDUNMAWAR 'YAN UNGUWA:
        Mutanen unguwa su dinga kakkafa kwamitoci domin hana yara sha da sayar da miyagun qwayoyi a unguwa.
5-GUDUNMAWAR QUNGIYOYIN SA KAI NA KOWAN GARI:
        Kowacce qungiya ta fito da wata hikima ta hana shaye-shaye a gari.
6-ILIMIN KOYAR DA ILLOLIN KAYAN SA MAYE YA ZAMA CIKIN TSARIN MANHAJAR KARATUN SAKANDARE
        Ya kamata ya zama cikin tsarin manhajar karatun sakandare, a sanya ilimin sanin illolin kayan sa maye a ciki, yin haka zai sa a shawo kan wannan matsala in-Sha-Allahu.


7-SAMAR DA AYYUKAN YI GA MATASA
        Akwai buqatar gwamnati ta samar da ayyukan yi, ta fuskar kafa masana'antu d.s. masu kuxi, da qungoyoyi, da sauran vangarorin jama'a, su bai wa gwamnati goyon baya, ta wajen samar da aikin yi ga matasa da koya musu sana'o'i.
8-KAKKAFA QANANAN MASANA'ANTU A BIRANE DA QAUYUKA
        Wannan zai sa kowanne matashi ya sami abin yi.
9-BAI WA HUKUMAR HANA SHA DA FATAUCIN MIYAGUN QWAYOYI (N.D.L.E.A.) HAXIN KAI WAJEN GUDANAR DA AIKINTA.
        Sau da dama idan 'yan wannan hukuma, suka shiga unguwa ko gari domin kama wani mai laifi 'yan unguwa sukan taru su hana a tafi da mai laifi, ko su je su yi, belinsa ko su hana hukunta shi, ko kuma a voye mai laifi a qi nuna shi. ya kamata a daina yin haka.
10- SHIRYA TARUKAN QARA WA JUNA SANI GA MATASA.
        A dinga shirya taron qara wa juna sani, ga limaman juma'a qungiyoyin xalibai, da na aikin gayya, masu koyar da darasin Addini a makarantu, da sauran muhimman mutane, su kuma su ci gaba da karantar da jama'arsu.
11-HUKUNTA MASU FATAUCI DA SHAN MIYAGUN QWAYOYI DA HUKUNCI MAI TSAURI.
        Idan muka duba qasar Saudi Arabiyya tana zartar da hukuncin kisa ga masu shigar musu da qwaya ko a jikin bizar shiga qasarsu ana rubutawa valo-valo, cewa duk wanda aka kama ya shiga da miyagun qwayoyi to, hukucin kisa ne.
12- QUNGIYOYIN LAFIYA DA MAKARANTUN KIMIYYA DA GWAMNATI, SU DINGA SHIGAR DA MASU MAGUNGUNAN MUSULUNCI CIKIN SHIRIN HANA SHA DA FATAUCIN MIYAGUN QWAYOYI:
13- ATSANANTA WAJEN HANA SHIGO DA KAYAN SA MAYE DAGA WAJE.
14-RABA MATASA DA BANGAR SIYASA.











(1) بريك عائض القرني، المخدرات الخطر الإجتماعي الداهم، ص:26، مجلد، دار ابن خزيمة سنة (1425-2005)
(1) العباسي، أسرار المخاطر التي تنتج...، مجلد، ص:102، جدة، سنة 2006م.
(2) المصدر السابق، ص:102.
(1)  M. Abbas A. Abbas (MNIM) Paper Presentation at Summit on Youths Drugs and Security 15/April, 2008 at Dutse Jigawa State Library Complex.