Saturday, 20 April 2013

MATSALOLIN MA'AURATA NA MUSAMMAN

GABATAR DA TAKARDA
DAGA
{DR.} YAKUBU MAIGIDA KACHAKO
MUKADDASHIN BABBAN KWAMANDAN HISBAH NA JIHAR KANO MAI KULA DA AIYYUKAN YAU DA KULLUM

MAI TAKEN
 مشاكل الزوجين الخاصة

MATSALOLIN MA’AURATA NA MUSAMMAN.

[SPECIAL PROBLEMS OF
COUPLES]


SHIMFIXA
MATSAYIN RASHIN LAFIYA GA XAN ADAM
Ita rashin lafiya Allah na sanyata a jikin xan-adam ne saboda abubuwa kamar haka:
1.     Qankarar Zunubai
Kamar yadda Allah ta’ala yake cewa:

((ما أصابكم من مصيبة فبما كسبت أيديكم ويعفو عن كثير)) [سورة الشورى: 30].
Ma’ana:
“Duk abin da ya sameku dangane da cutuka da masifu, na daga abin da kuka aiwatar da hannayenku, Ubangiji na yi muku rangwame akan abubwa masu yawa…”
"وما صييب المسلم من نصب ولا وصب ولا هم ولا أذى ولا غم حتى الشوكة يشاكها، إلا كفر الله من خطاياه". رواه البخاري.
Ma’ana:
Babu wani abu da zai sami muslumi na gajiya ko rashin lafiya ko damuwa ko wata cuta ko damuwa, ko da qayar da zai taka, face sai Allah ya kankare wani vangare na kura-kuransa (zunubai).
Don haka duk wanda Allah ya jarraba da wata cuta ko rashin lafiya, ana sa ran zunubansa ake kankare masa da ita.
2.     Xaukaka darajar mara lafiya da qara yawan ladansa.
Domin ya tabbata Manzon Alalh (S.A.W) ya ce:
"ما من مؤمن يشاك شوكة فما فوقها إلا كتبت له بها درجة ومحيت عنه بها خطيئة". رواه مسلم.
Ma’ana:
Babu wani mumini da zai taka qaya ko wani abin da ya darammata face sai an rubuta masa lada akan hakan, a kuma goge masa kurakurai.
3.     Tana zama sababin shigarsa aljanna.
"خفت الجنة بالمكاره وحفت النار بالشهوات". رواه البخاري ومسلم.
Ma’ana:
Aljanna an kewayeta da ababan qi, wuta kuma an kewayeta da ababan sha’awa.
Abinda ake nufi da (المكار) shi ne dukkan abinda rai baya so.
4.     Kuvuta ga barin shiga wuta:
Hadisi ya tabbata daga Abi Huraira (R.A) Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه عاد مريضا من وعك كان به فقال له: أبشر فإن الله عز وجل يقول: (هي ناري أسلطها على عبدي المؤمن في الدنيا، لتكون حظه من النار في الآخرة). أخرجه أحمد وغيره.
Ma’ana:
Manzon Allah (S.A.W) ya gaishe da wani marar lafiya wanda ke cikin zafin zazzavi sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi: (Ka yi farin ciki, domin Allah maxaukakni sari yana cewa; (Wuta tace da nake sanyata ga bawana mumini a rayuwarshi ta duniya, don ta kasance kasonsa na wutar lahira).
5.     Tunatar da bawa irin ni’imomin Ubangiji na baya da waxanda ake ciki.
6.     Tunatar da bawa iri halin da ‘yan uwansa marasa lafiya suke ciki.
7.     Tsarkake zuciya daga bari girman kai da jiji da kai.

No comments:

Post a Comment