Sunday, 14 December 2014

SIRRIN HANA MUTUWAR AURE





       GABATAR DA TAKARDA MAI TAKEN
SIRRIN HANA YAWAN MaCE-MACEN AURE.



   RANA:-         ASABAR (13/12/2014)


    LOKACI:-                     4:00 NA YAMMA


     GURI:     NASIRIYYA PRIMARY     SCHOOL     KWALABE KANO


    A YAYIN BIKIN AUREN HAJARA ADAMU HOTORO KANO


               2014=1436 A.H


GABATAARW
Allah Ta'ala Ya ce: 
فانكحوا ما طاب لكم من النساء مثني وثلاث ورباءفان خفتم ان لا تعدلوافواحدة.....
  النساء: ٣
Ma’ana: "Ku auri abin da ya yi muku dadi daga mataye ko  biyu, ko uku, ko hudu".
Sannan ya tabbata a sunnar Annabi (SAW) ya ce:-

  "تزوّجوا الودود الولود، فإنّي مكاثر بكم الأمم يوم القيامة
  رواه أحمد

  Ma'ana: "Ku yi aure na soyayya don ku hayayyafa, domin zan yi bugun-gaba da yawan al'umma a ranar alkiyama”.
  ZABAR MUJI
 Shara'ar Musulunci ta koyar da yadda ake   Zabar Muji.
  Dangane da fadin Manzon Allah (S.A.W).
 "إذا أتاكم من ترضون خلقه ودينه فزوّجوه إلاّ تفعلوا تكن فتنة في الأرض وفساد كبير
  رواه الترمذي وقال فيه حسن غريب.
*   Ma'ana: "Idan wanda kuka yarda da Halayensa da Addininsa ya zo neman Diyarku, to ku aura masa, in  ba ku yi hakan ba, fitina za ta faru a bayan kasa da barrna mai girma. 


§  SIFFOFIN MIJI NA GARI
      Mai Addini.
      Mai Ilimi.
      Mai Sana’a.
      Dan Dattawa.
      Mai iya mu’amala.
      Mai Tsabta.
      Mai Tausayi.
      Mai gaskiya da Amana.
      Mai cika alkawari.
      Mai iya soyayya.
      Mai rike sirri.
      NEMAN AURE
      1. Bin ka’idojin Addini yayin nema..
      2. Kada a kula juna
       3. kada a yi wa juna karya,
      4. Kada a yi dogon buri.
      5. Banda yaudara
      Ds.
§  TARIYA:
§  Akwai laduba da yakamata ma'aurata su sifantu da su.
*   An so idan ango zai shiga wajen amaryarsa ya yi abubuwa kamar haka:
*   Magana mai taushi,
*   Gabatar da wani abin ci ko sha.
*   Kamar yadda ya tabbata Manzon Allah (S.A.W) ya yi lokacin da zai tare da matarsa Assaiyida Aisha; sai ya shiga  da Nono a wani koko.
1.     Magana mai taushi,
2.    .       Gabatar da wani abin ci ko sha.
3.  SALLAH
§  An so Ango da Amarya su yi sallah ta nafila raka'a biyu a tare, domin an samu magabata na aiwatar da haka, kamar Asar din Abi Sa'idin Maula abi Asyad ya ce:
  "Na yi Aure ina Bawa, sai na gayyaci wani kaso na sahabban Annabi (SAW) a cikinsu akwai dan Mas'ud da Abu Zarin, sai ya yi nufin ya wuce, amma sai suka umarce ni da na wuce a matsayi na na Bawa,
  Suka kuma koyar da ni cewa:
  Dora hannu a goshin Amarya da yi  mata addu'a:
  Saboda Hadisin da ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) cewa:
   "إذا تزوج أحدكم امرأة، أو اشترى خادمًا، فليأخذ بنا ميتها، وليسم الله عزّ وجل، وليدع بالبركة، وليقل: "اللهم إنـّي أسألك من خيرها وخير ما جبلتها عليه، وأعوذ بك من شرها وشرما جبلتها عليه.
  SADUWA:
1.    Yin Addu'a – Saboda hadisin Bukhari:
2.    "بسم الله، اللهم جنّبنا الشيطان، وجنب الشيطان ما رزقتنا"
3.    Kada a sadu sai ta gaba.
4.    Yin wasannin motsa sha’awa.
5.    Yin wanka da zarar an gama.
6.    Raba tsakanin saduwa da alwala.
7.    Kada a sadu idan ana haila.
8.    Yin Addu’a kafin fara saduwa. 
MU KWANA A NAN.....

1 comment: