Sunday, 14 December 2014

SIRRIN HANA MUTUWAR AURE

       GABATAR DA TAKARDA MAI TAKEN
SIRRIN HANA YAWAN MaCE-MACEN AURE.

   RANA:-         ASABAR (13/12/2014)

    LOKACI:-                     4:00 NA YAMMA

     GURI:     NASIRIYYA PRIMARY     SCHOOL     KWALABE KANO

    A YAYIN BIKIN AUREN HAJARA ADAMU HOTORO KANO

               2014=1436 A.H

GABATAARW
Allah Ta'ala Ya ce: 
فانكحوا ما طاب لكم من النساء مثني وثلاث ورباءفان خفتم ان لا تعدلوافواحدة.....
  النساء: ٣
Ma’ana: "Ku auri abin da ya yi muku dadi daga mataye ko  biyu, ko uku, ko hudu".
Sannan ya tabbata a sunnar Annabi (SAW) ya ce:-

  "تزوّجوا الودود الولود، فإنّي مكاثر بكم الأمم يوم القيامة
  رواه أحمد

  Ma'ana: "Ku yi aure na soyayya don ku hayayyafa, domin zan yi bugun-gaba da yawan al'umma a ranar alkiyama”.
  ZABAR MUJI
 Shara'ar Musulunci ta koyar da yadda ake   Zabar Muji.
  Dangane da fadin Manzon Allah (S.A.W).
 "إذا أتاكم من ترضون خلقه ودينه فزوّجوه إلاّ تفعلوا تكن فتنة في الأرض وفساد كبير
  رواه الترمذي وقال فيه حسن غريب.
*   Ma'ana: "Idan wanda kuka yarda da Halayensa da Addininsa ya zo neman Diyarku, to ku aura masa, in  ba ku yi hakan ba, fitina za ta faru a bayan kasa da barrna mai girma. 

§  SIFFOFIN MIJI NA GARI
      Mai Addini.
      Mai Ilimi.
      Mai Sana’a.
      Dan Dattawa.
      Mai iya mu’amala.
      Mai Tsabta.
      Mai Tausayi.
      Mai gaskiya da Amana.
      Mai cika alkawari.
      Mai iya soyayya.
      Mai rike sirri.
      NEMAN AURE
      1. Bin ka’idojin Addini yayin nema..
      2. Kada a kula juna
       3. kada a yi wa juna karya,
      4. Kada a yi dogon buri.
      5. Banda yaudara
      Ds.
§  TARIYA:
§  Akwai laduba da yakamata ma'aurata su sifantu da su.
*   An so idan ango zai shiga wajen amaryarsa ya yi abubuwa kamar haka:
*   Magana mai taushi,
*   Gabatar da wani abin ci ko sha.
*   Kamar yadda ya tabbata Manzon Allah (S.A.W) ya yi lokacin da zai tare da matarsa Assaiyida Aisha; sai ya shiga  da Nono a wani koko.
1.     Magana mai taushi,
2.    .       Gabatar da wani abin ci ko sha.
3.  SALLAH
§  An so Ango da Amarya su yi sallah ta nafila raka'a biyu a tare, domin an samu magabata na aiwatar da haka, kamar Asar din Abi Sa'idin Maula abi Asyad ya ce:
  "Na yi Aure ina Bawa, sai na gayyaci wani kaso na sahabban Annabi (SAW) a cikinsu akwai dan Mas'ud da Abu Zarin, sai ya yi nufin ya wuce, amma sai suka umarce ni da na wuce a matsayi na na Bawa,
  Suka kuma koyar da ni cewa:
  Dora hannu a goshin Amarya da yi  mata addu'a:
  Saboda Hadisin da ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) cewa:
   "إذا تزوج أحدكم امرأة، أو اشترى خادمًا، فليأخذ بنا ميتها، وليسم الله عزّ وجل، وليدع بالبركة، وليقل: "اللهم إنـّي أسألك من خيرها وخير ما جبلتها عليه، وأعوذ بك من شرها وشرما جبلتها عليه.
  SADUWA:
1.    Yin Addu'a – Saboda hadisin Bukhari:
2.    "بسم الله، اللهم جنّبنا الشيطان، وجنب الشيطان ما رزقتنا"
3.    Kada a sadu sai ta gaba.
4.    Yin wasannin motsa sha’awa.
5.    Yin wanka da zarar an gama.
6.    Raba tsakanin saduwa da alwala.
7.    Kada a sadu idan ana haila.
8.    Yin Addu’a kafin fara saduwa. 
MU KWANA A NAN.....

Tuesday, 8 July 2014

MATAKAN KULA DA LAFIYA

GABATAR DA JAWABI AKAN MATAKAN KIWON LAFIYA A MUSLUNCI

MAI GATARWA:-

{DR.} YAKUBU MAIGIDA KACHAKO

DCG/OPS   KANO STATE HISBAH

RANA:- ASABAR  8/9/1435 AH=5/7/2014

 WURIN TARO:-  MAKARANTAR ALIYA KANO.

LOKACI:-   10:00 NA SAFE

                                                                2014

GABATARWA
Haqiqa an gaiyyace ni domin na gabatar da bayani akan MATAKAN KIWON LAFIYA A MUSLUNCI kuma an haxa ni da Malamina a matsayin shugaban zama, ko-da-yake ba a sanar da ni vangaren da ake so a kalla ba a kiwon lafiyar  to, sai de na zava wa kai na in xauki kiwon lafiya a matakin halittar Xan-adam.
 Ina roqon Allah ya ba ni ikon gabatar da wannan bayani cikin nasara.
Ba shakka Allah shi ya halicci Dan-Adam kuma ya fifita shi akan sauran halittu da abubuwa guda huxu:-

1.     Kirar jiki,
2.     Hankali,
3.     Ilimi, da kuma
4.     Shari’a
Ita kuwa shari’a an kawo ta ne domin ta kare wa dan-adam hakkoki guda biyar, su ne:-
1.     Hakkin Addini
2.     Mutunci,
3.     Dukiya
4.     Nasaba. da kuma
5.     Hakkin  Rai,
Wanda a qarqashinsa ne maganar kula da lafiya ta shigo.
Akwai girmamawa a cikin hlittar Mutum a cikin Mahaifa, da yadda ya tsara masa
Nakuda da haihuwa,  shayarwa, da kuma  rainon abin da aka haifa, da ba shi Tarbiyya.
SHIMFIXA
Ko shakka babu musulinci ya bayar da da cikakkiyar kulawa game da sha a nin kiwon lafiya, har ma masu iya Magana suna cewa:-
“Wato –Dirhami daya na riga kafi; ya fi Dirhamin neman magani alkhairi.”
              
Musulunci shi ne wanda ya fara sanya tubalin farko dangane da kiwon lafiya, a bi sa tsarin koyarwar manzon Allah [s.a.w]. Kamar yadda musulunci shi ne Addinin daya-xaya wanda ya zo da tsari tabbatacce wanda ya tsara cikin likitanci da kiwon lafiyar, Al’umma, kwatankwacin abinda ake kira a zamanin nan namu.
Imamu Tirmizii ya fitar da Hadisin Abu Hurayra, daga Annaabi [s.a.w] ya ce:-
“Farkon abin da za afara tambayar Bawa akansa na ni imomi a ranar  al’kiyama,  shi ne:- “shin ban inganta maka lafiyar jikinka ba? Na kuma shayar da kai daga ruwa mai sanyi”?....
An samo daga Al-imamu shafa’I, Allah yayi masa rahama yana cewa----
 “ Ilimi ya kasu kashi biyu:-
1. Ilimin Addini da za  a Bauta wa Allah ta’ala. da
2. Ilimin da za a kula da kiwon lafiytar jiki.
MA’ANAR  KALMAR  LAFIYA.
Malamai sun ba wa wannan kalma fassar iri-iri misali:-
1.      Kuvutar da jikin xan-adam daga kamuwa daga kocce irin cuta.
2.      Warkewa daga cuta jiki ya sami lafia.
MA’ANAR KIWON LAFIYA
Lafiya shine halin da dan-adam ke samun kansa na jin daxi ba tare da ya ci karo da kowacce irin cuta ko rashin lafiya ba, ya zama wajibi lafiya ta kasance abisa waxannan matakai kamar haka—
       I.            Lafiyayyen jiki
    II.            Lafiyayyen hankali
 III.            Lafiyayyun abokan zama
Ko shakka babu lafiya tana daga ma fi girman  Ni’imomi da Allah  ya yi  wa Dan- adam. Domin rayuwa ta arzuki tana da alaqa da kiwon lafiya. Saboda 

 MU KWANA A NAN.